A Karshe, Kwankwaso Ya Yi Magana kan Cire Sunan Aminu Gwarzo da INEC Ta Yi

A Karshe, Kwankwaso Ya Yi Magana kan Cire Sunan Aminu Gwarzo da INEC Ta Yi

  • Rabiu Kwankwaso ya yi fatan hukumar INEC za ta gyara kuskuren cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo
  • Kwankwaso ya ce jam’iyyar ta rubuta wa INEC wasiƙa kamar yadda hukumar ta buƙata, amma har yanzu ba ta samu amsa ba
  • Shugaban jam’iyyar na Kano ya ce INEC ta yi alƙawarin bincikar lamarin, kuma za ta iya mayar da sunayen ’yan takarar idan aka gano kuskure aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Rabiu Kwankwaso ya bayyana fatan cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta gyara cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo, daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan cire sunan Gwarzo daga jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta fitar kwanan nan.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

Aminu Gwarzo da Rabiu Musa Kwankwaso
Aminu Gwarzo a hagu da Rabiu Musa Kwankwaso a dama. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A hira da ya yi da Channels TV, Kwankwaso ya ce jam’iyyar da wakilanta sun tuntuɓi hukumar, wadda daga bisani ta nemi a rubuta mata wasiƙa.

Kwankwaso ya ce sun bi wannan umarni, amma har yanzu ba su samu amsa daga hukumar INEC ba.

Kiran Kwankwaso ga INEC

Kwankwaso ya bayyana cewa cire sunan Gwarzo ya jawo damuwa ga magoya bayan jam’iyyar, musamman a jihar Kano.

Ya ce:

“Ina so in sanar da magoya bayanmu, musamman na Kano, cewa ɗan takararmu na gwamna, mai girma Aminu Abdulsalam, abin takaici, INEC ba ta saka sunansa a jerin sunayen ’yan takara da ta fitar kwanan nan ba.
“Tabbas, jam’iyyar da wakilanmu sun je wajen hukumar, amma har yanzu ba a ba mu amsa ba. Sun nemi jam’iyyarmu ta rubuta musu wasiƙa, kuma mun yi hakan. Ina fatan INEC za ta gyara wannan kuskure.”
Yusuf Gawuna, Rabiu Kwankwaso da Aminu Gwarzo
Rabiu Kwankwaso a tsakiyar Aminu Gwarzo da Yusuf Gawuna. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

NDC ta ce INEC za ta yi bincike

Kara karanta wannan

"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Shugaban jam’iyyar NDC a Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ya bayyana cewa jam’iyyar ta kai ƙorafinta ga shugabancin ƙasa na jam’iyyar, wanda ya tuntuɓi INEC kan batun.

Ya ce hukumar ta yi alƙawarin gudanar da bincike domin gano ko an cire sunayen ’yan takarar ne bisa kuskure.

Daily Trust ta rahoto Mai Riga ya ce:

“Mun rubuta wa shugabancin ƙasa na jam’iyyarmu, kuma su ma sun miƙa lamarin ga INEC. Hukumar ta ce za ta bincika, kuma idan kuskure ne, za ta mayar da sunayen ’yan takararmu. Don haka yanzu muna jiran amsarta.”

Alakar Kwankwaso da Atiku

A wani rahoton, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso, ya yi kira ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya janye takararsa domin ya bai wa Peter Obi damar tsayawa takara a zaɓen 2027.

Kwankwaso ya ce kiransa ba ya nufin yana adawa da Atiku, wanda suka daɗe suna aiki tare a harkokin siyasa ƙarƙashin jagorancin marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua.

Ya kuma bayyana cewa sun yi aiki tare a lokuta daban-daban, ciki har da zaɓukan 1999, 2003 da 2011, sannan suka kasance cikin masu neman tikitin takarar shugaban ƙasa na APC gabanin zaɓen 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng