Mutanen Atiku Sun Gano Dabarar Kifar da Tinubu a Zaben 2027
- Jigon ADC, Dele Momodu ya ce jam’iyyarsu ta san dabarun da za ta bi domin hana Shugaba Bola Tinubu samun wa’adi na biyu a zaben 2027
- Momodu ya nuna shakku kan gudanar da sahihin zabe a karkashin Tinubu, yana zargin cewa wasu daga cikin magoya bayansa ma ba su son da haka
- Jigon ADC din ya kuma yi ikirarin cewa tsoron Tinubu ya sa wasu gwamnoni, alkalai da ’yan majalisa kasa kalubalantar shugaban kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta san dabarun da za ta yi amfani da su domin hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun wa’adi na biyu a zaben 2027.
Momodu ya bayyana hakan ne a wata hira a ranar Laraba, inda ya ce ’yan adawa na shirya matakan kalubalantar yunkurin Tinubu na sake lashe zabe.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Momodu ya ki bayyana dabarun da jam’iyyar ke shirin amfani da su, yana mai cewa ba za su fito fili su bayyana shirinsu ba.
Momodu: 'ADC ta samo dabaru'
Dele Momodu ya ce ba zai iya bayyana dabarun jam’iyyar a bainar jama’a ba, amma ya yi nuni da cewa Tinubu ma ya taba fuskantar kalubale wajen neman wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Legas.
Daily Post ta wallafa cewa Momodu ya ce:
“Ba zan iya gaya muku dabarunmu a bainar jama’a ba. Abin da muka sani shi ne, a wani lokaci, Tinubu ya yi gwagwarmaya domin samun wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Legas. Don haka, wasu ma suna aiki tukuru a bayan fage.”
Ya kara da cewa ba za su bayyana shirinsu a bainar jama’a ba, amma sun san abin da za su yi domin tabbatar da cewa Tinubu bai samu wa’adi na biyu ba.
Korafin Momodu kan INEC
Momodu ya kuma yi tambaya kan sahihancin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a karkashin gwamnatin Tinubu.
Ya yi zargin cewa shugaban kasar ya nada mutane da yawa daga Kudu maso Yamma a hukumar zaben, lamarin da a cewarsa ya jawo shakku kan yiwuwar gudanar da sahihin zabe a 2027.

Source: Facebook
Jigon ADC din ya ce idan aka tambayi ’yan Najeriya ko suna da yakinin cewa Tinubu zai tabbatar da gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci, yawancinsu za su ce a’a.
Momodu ya ce:
“Idan ka tambayi talakan Najeriya a yau game da Tinubu, ka amincewa da shi ya gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci? Zan iya gaya maka cewa kashi 90 cikin 100 za su ce a’a.”
Ya kara da cewa, a ra’ayinsa, hatta wasu daga cikin magoya bayan shugaban kasar ba su amince da shi wajen gudanar da sahihin zabe ba.
An ce Tinubu ba shi da lafiya
A wani labarin, kun ji cewa Kenneth Okonkwo ya yi tsokaci kan kalaman da aka danganta da Tinubu na cewa ba zai iya zagaya dukkan jihohin Najeriya domin yakin neman zabe ba.
Okonkwo ya yi ikirarin cewa shugaban kasar ba shi da lafiyar da zai iya gudanar da gagarumin yakin neman zaben shugaban kasa.
A cikin sanarwar, Okonkwo ya yi ikirarin cewa kalaman Gwamna Hope Uzodimma sun nuna cewa Tinubu zai ci gaba da gudanar da mulki daga ofishinsa.
Asali: Legit.ng


