Rokon da Gwamnatin Tarayya Ta Yi wa Atiku kan Takararsa da Tinubu a Zaben 2027

Rokon da Gwamnatin Tarayya Ta Yi wa Atiku kan Takararsa da Tinubu a Zaben 2027

  • George Akume ya bukaci Atiku Abubaar da yan siyasa su mutunta tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu
  • David Umahi ya bukaci ’yan Najeriya su sake zaben Bola Tinubu a 2027, yana mai cewa ci gaba da mulkinsa zai karfafa ayyukan raya kasa da gyaran tattalin arziki
  • Umahi ya kuma yabawa Gwamna Abba Yusuf kan tsaftar Kano, hadin kan al’umma da shugabanci nagari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya bukaci masu ruwa da tsaki a siyasa su mutunta tsarin karba-karban mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Ya ce tsarin na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiyar Najeriya, adalci da karfafa dimokuradiyya a kasar.

An bukaci Atiku da yan siyasa su bar Kudu da kammala wa'adinta
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Akume ya roki yan siyasa kan Tinubu

Akume ya bayyana hakan ne a jiya a Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Order of the Knights of St. Mulumba (KSM), reshen Najeriya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake bude hanyar Kano zuwa Zariya da Marigayi Buhari ya bude tun 2023

Tsohon gwamnan ya ce tsarin karba-karban mulki ya samo asali ne daga shawarwarin da shugabannin siyasa suka yi kafin komawar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999.

Ya bayyana cewa tsarin ya kasance muhimmin tsari wajen inganta hadin kan kasa da tabbatar da rabon karfin siyasa cikin adalci tsakanin yankunan biyu.

Akume ya ce manufar tsarin ita ce tabbatar da daidaito a siyasa, gina amincewa tsakanin yankuna da kare hadin kan Najeriya.

Ya kara da cewa tsarin zai hana wani yanki jin cewa an hana shi damar rike mukamin shugaban kasa har abada.

Akuma ya roki yan siyasa game da takarar Tinubu
Sakataren gwamnarin tarayya, George Akume. Hoto: Sen. Goerge Akume.
Source: Facebook

Muhimmancin amfani da tsarin karba-karba

Sakataren gwamnatin tarayyar ya jaddada cewa bai kamata a dauki tsarin karba-karban mulki a matsayin wata dabara ta siyasa ta wucin gadi ba.

A cewarsa, fahimtar siyasa ce ta asali wadda ta ginu bisa adalci, mutunta juna da tabbatar da zaman lafiyar kasa.

Ya kuma nuna damuwa kan yunkurin wasu ’yan takarar shugaban kasa daga Arewa na neman kujerar kafin kammala wa’adin mulkin Kudu na shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Tinubu zai fara karɓar harajin 25% daga kuɗaɗen shigan ƴan Najeriya?

Akume ya ce ya kamata a mutunta tsarin da aka amince da shi, maimakon a yi watsi da shi saboda muradun siyasa, cewar Punch.

Ya bayyana cewa bayan kammala wa’adin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas, ya kamata a bar shugaban kasa daga Kudu ya kammala nasa wa’adin.

A cewarsa, hakan zai tabbatar da bin tsarin musayar mulki tsakanin yankunan Arewa da Kudu.

Ya kara da cewa mutunta tsarin zai karfafa amincewar jama’a ga dimokuradiyya da kuma kyakkyawar fahimta tsakanin kungiyoyi da yankuna daban-daban na Najeriya.

APC ta musanta shirin hallaka Atiku

Mun ba ku labarin cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya yi magana kan zargin cewa akwai shirin kashe Atiku Abubakar.

APC ta buƙaci Timi Frank ya gabatar da hujjoji kan zargin, tare da kira ga hukumomin tsaro su gayyace shi domin gudanar da bincike.

Timi Frank ya nemi Donald Trump da sauran shugabannin ƙasashen duniya su sa baki kan zargin yunƙurin tsoratarwa da kama Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.