Akpabio Ya Bukaci Matasan Arewa Su Goyi Bayan Tinubu, Ya Kawo Dalilai
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman matasan Arewa, su goyi bayan sauye-sauyen tattalin arzikin Bola Tinubu
- Akpabio ya ce matakan da gwamnati ta dauka, ciki har da cire tallafin man fetur da gyaran tsarin musayar kudin waje, sun fara haifar da sakamako mai kyau
- Ya bayyana sauye-sauyen a matsayin matakai masu wahala amma wajibi domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya da kuma bude hanyoyin samun ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasan Arewa, da su goyi bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa.
Akpabio ya yi wannan kiran ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga ma su manyan mukamai daga Northern Ethnic Groups Assembly a gidansa da ke Abuja.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa kakakin kungiyar, Ibrahim Dan-Musa ya ce Akpabio ya ce cire tallafin man fetur da sauye-sauyen Tinubu na daga cikin matakan da suka kasance masu wahala amma wajibi domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Ribar sauye-sauyen Tinubu
Akpabio ya ce manufofin gwamnatin Tinubu sun riga sun tsallake wani muhimmin mataki, inda ake fara ganin alamun sakamako mai kyau.
“Ba na tsaye a gabanku a matsayin dan siyasa kawai ba, a’a, ina tsaye ne a matsayin ma’aikacin gwamnati da ya kuduri aniyar ganin Najeriya ta samu wadata, musamman wannan muhimmin yanki,”
In ji shi.
Batun cire tallafin man fetur
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce cire tallafin man fetur da kokarin da gwamnati ke yi na daidaita kasuwar musayar kudin waje na da muhimmanci wajen tabbatar da dorewar kudin gwamnati.
Premium Times ta wallafa cewa ya ce matakan za su taimaka wajen karkatar da albarkatun gwamnati zuwa muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi da samar da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan
Dan Majalisa ya kai ƙorafi gaban shugaban Amurka kan abin da ake wa Tinubu a Najeriya
“Duk da cewa wadannan matakai sun haifar da kalubale a farko, sun kasance kamar aikin tiyata da ake bukata domin karkatar da albarkatu zuwa kiwon lafiya, ilimi da abubuwan more rayuwa,”
In ji Akpabio.
Ya ce ana fara ganin alamun inganta tattalin arzikin kasar, ciki har da karuwar kudaden shiga na gwamnati, karuwar kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma sabunta sha’awar abokan hulda na kasa da kasa ga Najeriya.

Source: Twitter
Akpabio ya bukaci matasan Arewa su taka rawar gani wajen tafiyar da gwamnati da kuma ci gaban kasa tun yanzu, yana mai cewa bai kamata matasa su jira zuwa nan gaba ba.
'Yan siyasa sun fita daga APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu manyan jiga-jigan APC a jihar Bauchi sun yi murabus daga jam’iyyar duk da kokarin sulhu da Yakubu Dogara ke jagoranta.
Daga cikin wadanda suka fice akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar, Sagir Saleh, da tsohon mai neman takarar gwamna a karkashin APC har sau biyu, Bala Jibrin.
‘Yan jam’iyyar da suka nuna rashin gamsuwa sun zargi shugabancin APC da rashin adalci, rashin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyya da kuma zargin tilasta ‘yan takara.
Asali: Legit.ng
