Siyasa Ta Yi Zafi, Shettima Ya Yi wa Atiku Wankin Babban Bargo kan Taba Tinubu
- Sanata Kashim Shettima, ya soki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya ce rashin girmamawa ne ga Shugaba Bola Tinubu
- Shettima ya ce duk wanda ke neman shugabancin Najeriya ya kamata ya nuna ladabi, kamun kai da girmama hukumomin da kundin tsarin mulki ya kafa
- Ya kuma yi tambaya kan kudin da za a kashe wajen aiwatar da shawarar Atiku ta bayar da tallafi ga masana’antu, yana mai cewa hakan ba zai dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya bayyana a matsayin rashin girmamawa ga Shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya yi wannan jawabi ne ranar Laraba a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC na shekarar 2027, wanda aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Shettima ya ce duk wanda ke son zama shugaban Najeriya ya kamata ya nuna halayen da suka dace da mukamin tun kafin ya samu damar rike shi.
Shettima ya soki Atiku
Shettima ya ce duk da cewa Atiku na iya kiran shugaban kasar da sunan “Bola” ko “Adekunle”, hakan ba zai sauya gaskiyar cewa shi ne shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunonin sojin Najeriya ba.
Ya ce shi da kansa zai ci gaba da kiran Atiku da tsohon mataimakin shugaban kasa, yana mai cewa ba zai bi sahun Babachir Lawal wajen kiran Atiku da “Kachalla” ba.
Mataimakin shugaban kasar ya ce Atiku, wanda ya sha tsayawa takarar shugaban kasa har karo na takwas, ba kamar Abraham Lincoln ba ne, yana mai kwatanta shi da Oginga Odinga na Kenya.
Shettima ya bayyana cewa burin zama shugaban kasa ba ya ba dan siyasa damar yin watsi da ladabi da girmama hukumomin kasa.
Kiran Shettima ga 'yan takara
Shettima ya ce shugabancin Najeriya ba wata kujera ce ta siyasa kawai ba, illa shi ne babban mukamin da ke wakiltar ikon kundin tsarin mulki a kasar.
Ya ce wadanda ke neman wannan mukami dole ne su nuna kyawawan halaye da kuma sanin nauyin da ke kansu tun kafin a ba su damar jagorantar sama da ’yan Najeriya miliyan 200.
A cewarsa, girman mukamin da mutum yake nema yana kara nauyin da ya kamata ya dauka wajen zabar kalamansa, dabi’unsa da mu’amalarsa da hukumomin gwamnati.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ya kara da cewa burin siyasa ba wai kawai son samun mukami ba ne, domin yana bukatar mutum ya nuna karfin tunani, fahimta da kuma sanin ya kamata.
G-100 ta fara maganar hadaka
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyun adawa shida sun fara tuntubar ’yan takarar shugaban kasa a wani yunkuri na samar da hadin kai gabanin zaben 2027.
Tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman, ya ce tattaunawar ta kunshi shugabannin jam’iyyun da sakatarorinsu na kasa, kuma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.
Yunkurin na da nasaba da kudurorin taron G-100 na jam’iyyun adawa, wanda ya bukaci a karfafa hadin kai domin kare dimokuradiyya da muradun jama’a.
Asali: Legit.ng


