An Kwance Wa Kwankwaso Zani a Kasuwa da NNPP Ta Fadi Shirinta kan Zaben Babban 2027
- Jam'iyyar NNPP ta ce nan ba da jimawa ba za ta sanar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga wata jam'iyya da za ta marawa baya a zaɓen 2027
- Wanda ya kafa jam'iyyar, Dr. Boniface Aniebonam, ya ce za a gudanar da taron shugabannin jam'iyyar domin kammala shirin amincewa da ɗan takarar
- Aniebonam ya bayyana cewa NNPP za ta fi mayar da hankali kan zaɓen kujerun majalisa da na shugabancin jihohi a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta sanar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga wata jam'iyyar siyasa da za ta marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Uban jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Boniface Aniebonam, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za su zabi wanda suke ganin cancanta sannan su sanar da magoya baya.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, Aniebonam ya ce doguwar shari'ar da aka yi kan shugabancin jam'iyyar a matakin ƙasa ce ta jawo fashin tsaida dan takarar shugaban kasa a NNPP.
Ya bayyana cewa bayan Hukumar INEC ta amince da shugabancin NNPP ƙarƙashin jagorancin Dr. Agbo Major, jam'iyyar ta yi kokarin tsaida dan takara amma hakan ba ta faru b
NNPP ta yi nadamar tsaida Kwankwaso
Aniebonam ya ce NNPP ta tsaya tsayin daka kan manufofinta da ƙa'idojin da take buƙata daga duk wanda za ta marawa baya a takarar shugaban ƙasa.
Ya ce jam'iyyar ta yi kuskure a zaɓen 2023 da ta marawa Rabiu Musa Kwankwaso baya, kuma ba ta son sake yin irin wannan kuskuren.
“NNPP na nan kan manufofinta da ƙa'idojin da take buƙata daga ɗan takarar shugaban ƙasa. Mun yi kuskure da Kwankwaso a 2023, kuma ba ma son mu sake maimaita hakan,” in ji Aniebonam.
Yadda NNPP za ta zabi dan takara
Ya ƙara da cewa jam'iyyar ba ta matsu da neman mulkin Najeriya ko ta halin ƙaƙa ba, yana mai cewa Allah ne yake da ikon ƙarshe wajen zaɓar wanda zai jagoranci ƙasa.
“NNPP ba ta matsu da neman mulkin Najeriya ko ta halin ƙaƙa ba. Mun yi imani cewa Allah ne Yake bada mulki, kuma shi ne yake zaɓar wanda zai jagoranci ƙasa. Saboda haka, ra'ayinmu shi ne cewa siyasa ba batun dole sai an ci nasara ba ce,” in ji shi.

Source: UGC
Aniebonam ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyar na ƙasa za su yi taro nan ba da jimawa ba domin kammala dabarun amincewa da ɗan takarar, kafin su fitar da sanarwa a hukumance ga jama'a, cewar rahoton Vanguard.
Sunayen yan takarar shugaban kasa
Kun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fitar da jerin ’yan takarar shugaban ƙasa na karshe da za su fafata a babban zaben 2027.
Jerin, wanda Rose Oriaran-Anthony, Sakatariyar Hukumar INEC, ta sanya wa hannu, ya ƙunshi jam’iyyun siyasa 18 da ’ yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu.
Asali: Legit.ng

