Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Tsarin da 'Yan Najeriya Za Su Sayi Fetur da Arha
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a sayar da fetur mai rahusa a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30
- Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele ya ce masu motocin jigilar jama’a za su samu fifiko wajen cin gajiyar rangwamen
- Gwamnati ta kuma ce za a samu sabon tsarin farashin sauke fetur wanda za a rika duba shi duk wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ’yan Najeriya za su fara sayen fetur a farashi mai rahusa a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30.
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙin Ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026.

Source: Twitter
Za a rage farashin fetur na kwanaki 30
Oyedele ya bayyana cewa za a yi rangwame kan farashin fetur da ake sayarwa a gidajen mai na NNPCL na tsawon kwanaki 30, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce masu motocin jigilar fasinjoji za su samu fifiko wajen cin gajiyar wannan rangwame.
Ministan ya ce, “Za a yi rangwame kan fetur na NNPC na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar jama’a fifiko.”
Za a rika duba farashin duk wata
Oyedele ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta samar da wani sabon tsarin farashin sauke fetur da aka cimma ta hanyar tattaunawa.
A cewarsa, za a rika duba wannan farashi duk wata domin tabbatar da cewa tsarin ya dace da yanayin kasuwar man fetur.
Ya ce gwamnati za ta samu “farashin sauke fetur da aka cimma ta hanyar tattaunawa, wanda za a rika duba shi duk wata”. Cikakkun bayanai kan sabon farashin fetur da yadda za a aiwatar da rangwamen ana sa ran za su fito daga baya.
Ku dakaci karin bayani....
Asali: Legit.ng
