Wata Sabuwa: APC Ta Samo Alkaluman da Suka Nuna Wanda zai Ci Zaben 2027
- Jam'iyyar APC mai mulki ta sake jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ne zai samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
- Shugaban Jam’iyyar, Nentawe Yilwatda, ya ce binciken cikin gida da alƙaluman da suka tara sun nuna cewa Tinubu yana gaba da kowa
- Yilwatda ya ayyana cewa APC ba ta tsoron 'yan adawa saboda rashin nasarar da jam'iyyun ADC da NDC suke samu yana ba APC babbar dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya cika baki da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyu ke cigaba da shiri domin neman jama'a su goyi bayansu a zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Twitter
Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana cewa jam'iyyar ta gudanar da bincike na zahiri a faɗin jihohin ƙasar.
APC: "Muna da ingantattun alƙaluma"
Yayin da ya ke nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027, Yilwatda ya jaddada cewa:
"Mun yi binciken gano gaskiya, kuma mu ne a gaba. Mun gudanar da binciken ra'ayin jama'a na kanmu wanda ya ba mu ingantattun alƙaluma a faɗin jihohi."
Yayin da aka tambaye shi ko alƙaluman sun nuna Tinubu zai yi nasara akan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na ADC da Peter Obi na NDC, ya amsa da cewa:
"Ƙwarai kuwa!"
'Haraji ya taimaki talaka' in ji APC
Shugaban na APC ya ƙara da cewa tsarin harajin da Tinubu ya ƙaddamar yana taimakawa mutane mafi talauci a ƙasar, sannan tsadar rayuwa da na man fetur da ake ciki a yanzu abubuwa ne na wucin gadi da za su wuce.
A martaninsa kan zargin cewa jam'iyyar tana kare mambobinta daga tuhumar cin hanci da rashawa, Yilwatda ya ƙaryata hakan da cewa babu wanda ake ba kariya a APC.
Batun 'yan 'Tinubu-Must-Go'
Dangane da masu fafutukar TTinubu Must Go, Yilwatda ya watsar da buƙatunsu inda ya bayyana su a matsayin 'yan adawa kawai wadanda ba su wakiltar 'yan Najeriya.
A jiya Lahadi ne 'yan sanda suka tarwatsa masu taron 'Tinubu Must Go' a garin Kano, inda jami'an tsaron suka bayyana cewa sun shiga tsakani ne domin tsaro da kariya ga jama'a.

Source: Facebook
APC ta yi magana kan Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban APC na Ƙasa, Prof. Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa ba ya adawa da duk wanda yake son ba Shugaba Bola Tinubu goyon baya, har da ƙungiyar 'Rainbow Coalition' da Nyesom Wike, ya ƙirƙira.
Wike ne ke jagorantar wannan ƙungiya domin tara goyon baya ga Tinubu a zaɓe mai zuwa, koda yake matakin ya haifar da samun sa-in-sa tsakanin ministan da gwamnonin jam'iyyar APC.
Yilwatda ya tabbatar da cewa matsayar jam'iyyar tana tafiya kafada da kafada da ra'ayin gwamnonin jihohi wajen haɗa kai domin nasarar shugaban ƙasar.
Asali: Legit.ng

