Pantami: INEC Ta Yi Magana kan 'Yan Takara a Gombe, Kano da Jihohi 4

Pantami: INEC Ta Yi Magana kan 'Yan Takara a Gombe, Kano da Jihohi 4

  • INEC ta karyata wata sanarwa da ke yawo a intanet kan matsalolin jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohin Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da Kano
  • Hukumar ta bayyana sanarwar a matsayin ta bogi, tare da gargadin jama’a da su guji yadawa, su rika dogaro da bayanan da aka wallafa a tashoshinta na hukuma
  • Wannan na zuwa ne bayan rashin sunan dan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, da wasu 'yan takara a Gombe, da sauran jihohin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar INEC ta karyata wata sanarwa da ke yawo a kafafen intanet, wadda ke ikirarin cewa hukumar ta fitar da sanarwa ta musamman kan matsalolin da suka shafi jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohi shida.

Kara karanta wannan

'Yan Kwankwasiyya a Kano sun tafi ofishin INEC kan cire sunan Aminu Gwarzo

Jihohin da sanarwar ta ambata su ne Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da Kano.

Shugaban INEC a Najeriya
Takardar bogi da INEC ta karyata. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A cikin sanarwar da ta fitar a Facebook, INEC ta bayyana cewa sanarwar bogi ce kuma ba ta fito daga hukumar ba, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da ita, kada su ci gaba da yadawa.

INEC ta gargadi kan sanarwar bogi

Hukumar ta bayyana cewa babu wata sanarwa ta musamman da ta fitar kan ’yan takarar gwamna a jihohin da aka ambata, kamar yadda sakon da ke yawo a intanet ya nuna.

Ta bukaci jama’a su rika tantance sahihancin bayanan zabe kafin su yada su, domin guje wa fadawa tarkon masu yada labaran karya.

INEC ta ce ya kamata jama’a su dogara da sanarwa, takardun manema labarai da sauran bayanan da aka wallafa ta shafukanta na hukuma kawai.

Daga cikin hanyoyin samun sahihan bayanai akwai shafin hukumar na www.inecnigeria.org, shafinta na Facebook mai suna INEC Nigeria, da kuma shafukan X da Instagram mai suna @inecnigeria.

Kara karanta wannan

PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara

Hukumar ta kuma ambaci shafin labaranta na www.inecnews.com.

Hanyoyin tuntubar INEC

INEC ta kuma bayyana hanyoyin da jama’a za su iya bi domin neman karin bayani ko yin tambayoyi kan harkokin zabe.

Hanyoyin sun hada da cibiyar kiran hukumar ta 0700-2255-4632, gajeren lambar waya ta 4632, da lambobin waya 090844444333 da 09050858629.

Wajen zabe a Anambra
Mutane a wajen kada kuri'a a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Haka kuma, jama’a na iya aika sakon imel zuwa iccc@inec.gov.ng ko ziyartar shafin hukumar na www.inecnigeria.org domin samun bayanai.

Hukumar ta sake jaddada cewa tana da niyyar sanar da jama’a sahihan bayanai, tare da kira ga kowa da kowa da ya yi watsi da sanarwar bogin.

Korafin Kwankwasiyya ga INEC

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci INEC ta yi bayani kan rashin sunayen Aminu Gwarzo da mataimakinsa a jerin ’yan takarar gwamnan Kano.

Kakakin kungiyar, Dr Habibu Sale Mohammed, ya ce lamarin ya jawo damuwa ga magoya baya, amma ya bukaci su guji yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Kwankwasiyya ta yi kira ga INEC da ta bayyana dalilin rashin sunayen ’yan takarar, tare da shawartar jam’iyyar da lauyoyinsu su tattara takardun rajista da na tsayar da ’yan takara domin neman warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng