Tallafin Tinubu Gida Gida, Dubban Dalibai Za Su Sake Samun Taimakon Kudi
- Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta sanar da shirin bai wa ɗalibai 100,000 tallafi domin rage matsalolin kuɗin karatu
- Ta ƙaddamar da rabon fakitin kayan tsaftar jinin al’ada miliyan biyu da kayan karatu ga ’yan mata a makarantun gwamnati
- Ministan Ilimi ya ce gwamnati za ta sanya shirin cikin kasafin kuɗin shekara, yayin da jami’ai suka buƙaci a tabbatar da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa bai kamata a hana wata yarinya ’yar Najeriya damar yin karatu ba.
Oluremi ta ce ya kamata kowace ta cimma burinta inda ta yi magana kan matsalolin tsaftar jinin al’ada ko rashin kuɗin a cikin iyali.

Source: Facebook
Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da rabon fakitin kayan tsaftar jinin al’ada miliyan biyu da kayan karatu ga ’yan mata, cewar Punch.
Oluremi ta kaddamar da tallafi ga dalibai
Uwargidan shugaban kasar ta kaddamar da hakan ne a makarantun firamare da ƙananan sakandare na gwamnati, a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ta kuma sanar da shirin tallafin riƙe ɗalibai a makaranta na Naira biliyan biyu, wanda zai fara da ɗalibai 100,000.
Ana sa ran kowane ɗalibi zai samu N20,000 domin taimaka masa shawo kan matsalolin kuɗi da ke hana zuwa makaranta ko ci gaba da karatu.

Source: Twitter
Dalilin kaddamar da tallafin Oluremi ga dalibai
A yayin taron, Oluremi Tinubu ta ƙaddamar da rabon fakitin kayan tsaftar jinin al’ada miliyan biyu da kayan karatu ga ’yan mata a makarantun gwamnati a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.
Ta ce an tsara tallafin ne domin kawar da matsalolin da ke tilasta wa ’yan mata, musamman waɗanda ke yankunan karkara, rashin zuwa makaranta lokacin da suke jinin al’ada.

Kara karanta wannan
Kakar miliyoyin matasa ta yanke saƙa, an fadada shirin tallafin rage talauci a Najeriya
Ta ce:
“Domin mu tabbatar da cewa ’yan matanmu sun ci gaba da zuwa makaranta, dole ne mu gane tare da magance matsalolin da ke shafar karatunsu, musamman waɗanda ke yankunan karkara, waɗanda galibi ba sa zuwa makaranta saboda rashin kayan tsaftar jinin al’ada.”
Ta ce shirin farko ya samar da kayan tsaftar jinin al’ada da za su wadaci ’yan mata 370,000 na tsawon shekara guda a yankunan karkara a faɗin ƙasar, cewar Vanguard.
Oluremi ta buƙaci matan gwamnonin jihohi, kwamishinonin ilimi da shugabannin hukumomin ilimin firamare da ƙananan makarantu na jihohi su tabbatar da cewa kayan sun isa ga waɗanda aka yi niyyar tallafawa, cikin gaskiya da riƙon amana.
Oluremi ta roki al'umma kan zaben Tinubu
An ji cewa uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta roƙi ’yan Kudu maso Gabas su sake zaɓar mijinta, Bola Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Oluremi Tinubu ta ce tana son ganin Najeriya ta inganta kafin ta tsufa, yayin da ta bayyana cewa ita da shugaban ƙasa suna aiki don cigaban ƙasar.
Uwargidan shugaban ƙasar ta ƙarfafa mata 2,500 a Imo da kayan sana’a, sannan ta sanar da ƙarin tallafin N100,000 ga kowacce daga cikin waɗanda suka amfana.
Asali: Legit.ng
