Wani Mutumi Ya Nufi Fadar White House Zai Kashe Shugaban Kasar Amurka

Wani Mutumi Ya Nufi Fadar White House Zai Kashe Shugaban Kasar Amurka

  • Jami’an tsaron Amurka sun kama wani dan kasar Venezuela kusa da Fadar White House bisa zargin yin barazanar kashe Shugaba Donald Trump
  • An gano bindiga kirar rifle guda daya da kananan bindigogi guda biyu tare da alburusai da dama a cikin motar da yake ciki
  • Wanda ake zargin ya shaida wa jami’an cewa wasu muryoyi a cikin kansa sun umarce shi da ya je Washington domin kashe Trump

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Jami’an Hukumar Tsaron Amurka (US Secret Service) sun kama wani mutum kusa da Fadar White House a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, 226.

Jami'an tsaron sun kama mutumin ne bisa zargin yana dauke da bindigogi da dama a cikin motar da aka sace, kuma ya yi barazanar kashe Shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan

Matashi ya dauki bindigogi da niyyar kashe Trump a Amurka

Shugaban Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Tashar CNN ta rahoto cewa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta tabbatar da kama mutumin a kusa da fadar White House a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Yadda aka kama mutumin a Amurka

Ta ce jami’an tsaron sun lura da mutumin mai suna Ronny Yordrix Guanipa Chrinos, dan kasar Venezuela, yana aikata abubuwan da suka sanya su zarginsa a cikin wata mota kusa da Fadar White House.

Ma’aikatar ta ce Chrinos ya shiga Amurka ba bisa ka’ida ba. DHS ta ce lokacin da jami’an suka tunkare shi domin yi masa tambayoyi, ya ce wasu muryoyi a cikin kansa ne suka gaya masa ya je Washington, D.C., domin kashe Shugaba Trump.

Sanarwar ta ce:

“Lokacin da jami’an suka tunkari wanda ake zargin, ya ce ya ji wasu muryoyi a cikin kansa suna gaya masa ya zo Washington, D.C., domin kashe Shugaba Trump.
"Daga nan jami’an suka gano cewa an riga an sanar da satar motar da yake ciki, sannan wanda ake zargin ya amince cewa akwai makamai a cikin motar.”

Kara karanta wannan

Zabe ya wuce, Trump na shirin kaddamar da manyan hare hare Iran

An gano bindigogi da alburusai

DHS ta ce jami’an sun gano bindiga guda daya da kananan bindigogi guda biyu, tare da alburusai da dama a cikin motar, kamar yadda NBC News ta ruwaito.

An kama Chrinos bisa zarge-zargen mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, amfani da abin hawa ba tare da izini ba da kuma karbar kayan sata.

A yanzu haka yana hannun Hukumar Kula da Fursunoni ta Amurka (US Marshals Service). DHS ta ce Chrinos ya shiga Amurka ba bisa ka’ida ba a shekarar 2024.

White House.
Fadar White House da ke birnin Washington D.C na kasar Amurka Hoto: Kevin Carter/Getty Images
Source: Getty Images

Darakta-Janar na Hukumar Tsaron Amurka, Sean Curran, ya ce jami’ansu sun yi amfani da horo da kwarewarsu wajen shawo kan lamarin ba tare da kara tsananta shi ba.

Ya ce:

“Wannan shi ne sabon misali na yadda jami’an Secret Service ke amfani da horo da kwarewa wajen kwantar da hankalin wani mutum da ke cikin yanayi mai hatsari, wanda ya kasance barazana ta kusa ga mutanen da muke karewa da sauran Amurkawa.

Kara karanta wannan

Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano

Trump na shirin sake yakar Iran

Kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya gana da jami’an tsaron ƙasarsa domin tattauna yiwuwar sake fara hare-haren soji kan Iran.

Jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa an gudanar da tarurruka a fadar White House a ranakun Laraba da Alhamis domin duba matakin da ya kamata a ɗauka kan rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262