Akpabio Ya Fadi Miliyoyin Kuri'un da zai Samawa Tinubu a 2027

Akpabio Ya Fadi Miliyoyin Kuri'un da zai Samawa Tinubu a 2027

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi alkawarin cewa jihar Akwa Ibom za ta samar wa Tinubu kuri’u sama da miliyan biyu a zaɓen 2027
  • Gwamnan jihar, Umo Eno, da sarakunan gargajiya sun sake tabbatar da goyon bayansu ga shugaba Tinubu da ya ziyarci jihar
  • Akpabio ya bayyana Tinubu a matsayin jagora mai hangen nesa, tare da cewa ’yan majalisa za su ci gaba da mara wa gwamnatinsa baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Akwa Ibom – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi alkawarin cewa jihar Akwa Ibom za ta samar wa Shugaba Bola Tinubu kuri’a sama da miliyan biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sanata Akpabio ya bayyana hakan ne a wani liyafar cin abinci da aka shirya domin karrama Tinubu yayin ziyarar da ya kai jihar.

Kara karanta wannan

An bayyana tulin ayyukan alherin Tinubu a Arewa da ya cancanci tazarce a 2027

Godswill Akpabio a majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

A cewar rahoton VON, Gwamna Umo Eno da sarakunan gargajiya na jihar sun kuma tabbatar da goyon bayansu ga shugaban ƙasar, inda suka yaba da manufofin gwamnatinsa da ayyukan raya ƙasa.

Akpabio ya yabi Tinubu

A yayin jawabin nasa, Akpabio ya bayyana Tinubu a matsayin mutum mai gaskiya, hangen nesa da kuma aiwatar da manufofinsa.

Ya ce tun lokacin da yake matashi kuma yana aiki a Legas, ya lura da tsarin shugabancin Tinubu lokacin da yake gwamnan jihar, lamarin da ya sa ya yi burin yin koyi da shi idan ya samu damar mulki.

Akpabio ya ce Tinubu ya faɗaɗa wannan hangen nesa zuwa matakin ƙasa, inda ya bayyana cewa Najeriya na sauyawa saboda salon shugabancinsa.

Ya kuma kawo cire tallafin man fetur, aikin hanyar bakin teku da ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a matsayin misalan manufofin da Tinubu ya aiwatar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya na yi wa 'yan kasa bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaban Majalisar Dattawan ya tabbatar wa Tinubu cewa Majalisar Tarayya za ta ci gaba da mara wa gwamnatinsa baya, yana mai cewa gwamnonin Kudu maso Kudu ma sun daidaita kansu da manufofinsa na raya ƙasa.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Punch ta wallafa cewa Akpabio ya kuma yi wa shugaban ƙasar alkawarin cewa ba zai rasa goyon bayan mutanen Akwa Ibom ba har zuwa ƙarshen wa'adinsa a 2031.

Gwamna Eno ya gode wa Tinubu

A nasa jawabin, Gwamna Umo Eno ya gode wa Tinubu bisa cika alƙawarin ziyartar jihar Akwa Ibom da kuma amincewa da aikin tashar jirgin ruwa ta Ibom.

Eno ya tuna cewa lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan yiwuwar ziyarar shugaban ƙasar, Tinubu ya tabbatar masa cewa zai cika alƙawarinsa.

Gwamnan ya kuma ce kuɗin da gwamnatin tarayya ta saki ga jihohi sun taimaka wa gwamnatinsa wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Shettima ya caccaki Obi

A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya zargi Peter Obi da lalata damar siyasarsa ta zaɓen 2027 ta hanyar yaɗa bayanan da ya bayyana a matsayin ƙarya da alkaluma marasa tushe.

Shettima ya ce Obi, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar NDC, ya rasa farin jinin da yake da shi a baya, kuma kalamansa ba sa burge ’yan Najeriya kamar yadda ya saba.

Mataimakin shugaban ƙasar ya yi waɗannan kalamai ne a wajen wani gangamin jam'iyyar APC da aka gudanar a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng