Zaɓen 2027: Kashim Shettima Ya Shiga Ganawar Sirri da Tosaffin Gwamnoni

Zaɓen 2027: Kashim Shettima Ya Shiga Ganawar Sirri da Tosaffin Gwamnoni

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gana da wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni a Najeriya ana shirin zaben 2027
  • Taron ya samu halartar wasu jiga-jigan siyasa, ciki har da Simon Lalong da Buba Marwa, yayin da ba a bayyana cikakken dalilin ganawar ba
  • Ganawar ta zo ne gabanin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ranar 14 ga Oktoba, kafin fara kamfen a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, yana gudanar da ganawar sirri da tsofaffin gwamnoni a Najeriya.

Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, tsohon gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, da sauran ’yan siyasa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shettima ya gana da tsofaffin gwamnoni
Mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Tawagar, wadda aka bayyana a matsayin shugabannin National Directorate of Arewa for Asiwaju Movement, ta isa Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, sannan ta nufi sashen ofishin mataimakin shugaban ƙasa, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

2027 da magana: Dubban mutane sun yi gagarumin gangami a Arewa saboda Tinubu

Sai dai a lokacin da tawagar ta isa, Shettima yana halartar wani taro na daban a sashen ofishin shugaban ƙasa, wanda aka fara da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Taron farko ya samu halartar Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Maiha, da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman, kuma mai kula da Shirin Gyaran Kiwo na Shugaban Ƙasa, Farfesa Attahiru Jega, tare da wasu jami’ai.

Jega tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ne.

Ko da yake ba a bayyana dalilin ziyarar tawagar nan take ba, bayanai sun nuna cewa ganawar ziyarar girmamawa ce.

An yi ganawar sirri tsakanin Shettima da tsofaffin gwamnoni
Taswirar birnin tarayya Abuja. Hoto: Legit.
Source: Original

Sauran waɗanda suke Fadar Shugaban Ƙasa sun haɗa da tsohon gwamnan Plateau, Simon Lalong, da Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan daidaita manufofi, Hadiza Bala-Usman.

Ganawar ta zo ne kwanaki biyu kafin bikin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, wanda aka shirya gudanarwa ranar Laraba, 14 ga Oktoba, a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

2027: Arewa ta shirya gagarumin gangamin tallata Tinubu da Shettima

Haka kuma, ganawar ta gudana ne gabanin fara kamfen ɗin jam’iyyar a Jihar Kaduna, wanda aka tsara gudanarwa ranar 24 ga Oktoba, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen, Sanata Abdulaziz Yari, ne ya sanar da ranakun ga manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa ranar Juma’a, bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar.

Yari ya bayyana cewa bayan fara kamfen a Kaduna, za a kai kamfen ɗin zuwa Fatakwal da Maiduguri. Ya ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin kamfen bayan ƙaddamar da kwamitin.

Tinubu na neman sake lashe zaɓen shugaban ƙasa, wanda aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairu, 2027.

An yi gangamin goyon bayan Tinubu, Shettima

A wani labarin, an ji cewa jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiya ta shirya gudanar da gagarumin gangami a Lafia domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu.

Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce za a tattara magoya baya daga jihohi shida da Abuja.

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, zai halarci taron da uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.