An Hango Shettima a Gona a Kasar Habasha, Ya Fadi Alherin da zai Kawo Najeriya

An Hango Shettima a Gona a Kasar Habasha, Ya Fadi Alherin da zai Kawo Najeriya

  • Kashim Shettima ya bayyana cewa Najeriya za ta yi amfani da tsarin bunƙasa aikin noma na yankin Oromia da ke ƙasar Habasha domin tabbatar da wadaratar abinci
  • Shettima ya gargaɗi cewa ƙasar da ta dogara da wasu wajen ciyar da al'ummarta tana fuskantar barazana ga 'yancinta da ikonta na ƙasa a nan gaba
  • Najeriya ta tsara kaddamar da shirin dasa bishiyoyi biliyan 20 a muhalli a lokacin damina mai zuwa sakamakon koyi da tsarin kiyaye muhalli na Habasha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Addis Ababa – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da babban shirin gina manyan ayyukan kyautata aikin noma domin magance matsaloli a harkar adana da rarraba amfanin gona tare da faɗaɗa arzikin ƙasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Senator Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa rangadin gona da cibiyoyin aikin noma a yankin Oromia na ƙasar Habasha a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Bayan hadarin Ondo, jirgin sojin Najeriya ya sake samun matsala a sama

Kashim Shettima a gona
Lokacin da Kashim Shettima ya ziyarci wata gona a Habasha. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Stanley Kingsley Nkwocha ya wallafa a Facebook cewa Shettima ya bayyana tsarin Oromia a matsayin madubi da ya kamata sauran ƙasashen Afrika su yi koyi da shi domin samar da sauyi mai ɗorewa a harkar noma.

Noma: Shettima ya yabi Habasha

Shettima ya yabawa ƙasar Habasha bisa yadda ta koma samar da alkama da kanta a maimakon kashe dalar Amurka biliyan 1 wajen shigo da ita a kowace shekara, har ma ta fara fitarwa zuwa ƙasashe makwabta irinsu Djibouti da Kenya.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa:

"Rasa 'yancin ciyar da kai yana tauye cin gashin kai na kowace ƙasa. Balle 'yancin samar da abinci, babu wata ƙasa da za ta iya cewa tana da cikakken ikon kanta idan ba ta samar da abincin da za ta ci."

Shirin Dasa Bishiyoyi Biliyan 20

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana aniyar Najeriya na ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi biliyan 20 a lokacin damina mai zuwa sakamakon koyi da shirin 'Green Legacy Initiative' na Habasha wanda ke haɗa kiyaye muhalli da bunƙasa tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan tsadar kayan noma, ya fadi mafita tare da sukar Tinubu

A cewar Shugaban Yankin Oromia, Shimelis Abdisa, noman alkama kaɗai yana samar wa Habasha sama da dalar Amurka biliyan 3.1 a kowace shekara, sannan yankin yana haɗin gwiwa da kamfanin Dangote wajen samar da takin zamani ga manoma.

Kashim Shettima a gona
Kashim Shettima a gonar alkama. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Tawagar ta gudanar da ziyarar gani da ido zuwa gonakin alkama, abarba da Inabi a yankin domin fahimtar hanyoyin da ake amfani da su wajen haɓaka aikin noma.

An tallafawa mata a Kastina

A wani labarin, mun ruwaito cewa mata sama da 40,000 a jihar Katsina ne za su amfana da tallafin asusun zuba jari ƙarƙashin shirin tallafi biyo bayan fara raba kuɗi ga ƙungiyoyi a Katsina.

Yayin da yake jawabi a taron ƙaddamar da rabon kuɗin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa shirin zai bunkasa tattalin arzikin mata.

Shettima ya jaddada cewa mata waɗanda za su amfana sun nuna sun samu kyakkyawan horo wajen adana kuɗi da gudanar da ayyukan ƙungiyoyinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng