Ya Mutane Za Su Samu Fetur Mai Araha a Garuruwan da Babu Gidan Man NNPC? An Aika Sako ga Tinubu
- Hadimin Atiku Abubakar ya ce shirin rage farashin fetur na kwanaki 30 ba zai wadatar wajen rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa ba
- Paul Ibe ya ce ƙarancin gidajen mai na kamfanin NNPC a sassa daban-daban na ƙasar zai hana mutane da dama amfana da shirin
- Ibe ya jaddada cewa rage farashin fetur dole ne ya zama mai sauƙin samu, adalci ga kowa da kuma wanda za a iya dorewa da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mai ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya soki shirin gwamnatin tarayya na rage farashin fetur na tsawon kwanaki 30.
Hadimin Atiku ya bayyana cewa shirin ba zai sauƙaƙa wa ’yan Najeriya rayuwa yadda ya kamata ba saboda ƙarancin gidajen sayar da man fetur na kamfanin NNPC.

Kara karanta wannan
Bayan fetur, Gwamnatin tarayya na shirin rage hauhawar farashin muhimman kayayyaki

Source: Twitter
Ibe, wanda ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, ya ce ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa fetur ya zama mai sauƙin saya a faɗin ƙasar.
“’Yan Najeriya suna buƙatar sauƙi, ba surutu ba,” in ji shi, inda ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da mayar da hankali kan gardama maimakon magance matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta.
Duk da cewa ya yi maraba da duk wani sahihin matakin rage farashin fetur, Ibe ya dage cewa dole ne a tabbatar da cewa rage farashin ya kasance bisa adalci, mai sauƙin samu ga jama’a kuma mai ɗorewa.
Ƙarancin gidajen mai ma NNPC
Ibe ya bayyana cewa ƙarancin gidajen sayar da man fetur na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) a sassan ƙasar zai hana ’yan Najeriya da dama cin gajiyar shirin.
A cewarsa, Najeriya tana da kusan gidajen mai 22,681, yayin da NNPC ke da fiye da 900 kacal, adadin da ya kai kusan 4% na dukkan gidajen fetur a ƙasar.
Ya ƙara da cewa kaso 17% na kasuwar fetur a matakin dillalai na NNPC ne a shekarar 2024, yayin da rahoton kamfanin na Yuli 2026 ya nuna cewa ana samun fetur a kashi 52% na gidajen man da yake gudanarwa.
Taya mutane za su amfana da shirin?
Ibe ya aika sakon tambaya ga gwamnati kan wannan tsari, inda ya ce:
“Ta yaya gwamnati za ta samar da sauƙi mai ma’ana ga ’yan Najeriya a faɗin ƙasar ta hanyar amfani da gidajen man da babu su a ko'ina? Wanda kuma aka san ba ko yaushe ake samun mai ba."
Ya kuma tambayi abin da zai faru da ’yan Najeriya da ke zaune a garuruwan da babu gidajen man NNPC, yana mai cewa dole su yi tafiya mai nisa tare da kashe ƙarin kuɗi domin amfana da rangwamen.

Source: Getty Images
Hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi gargaɗin cewa tsarin na iya haifar da rashin daidaito wajen samun fetur mai sauƙin farashi.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Atiku zai inganta harkokin noma
A wani labarin, kuj ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza tallafa wa manoma.
Ya ce idan ya samu damar kafa gwamnati, zai dawo da wani tsari na tallafin samar da man fetur a cikin gida daga ranar farko, tare da tallafa wa manoma da masu sarrafa amfanin gona.
Asali: Legit.ng
