2027 da Magana: Dubban Mutane Sun Yi Gagarumin Gangami a Arewa saboda Tinubu
- Jam’iyyar APC ta gudanar da gangamin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027
- Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, da Gwamna Abdullahi Sule sun halarci gangamin tare da George Akume
- Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta jagoranci tawagar mata daga jihohi shida na Arewa ta Tsakiya zuwa gangamin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Jam’iyyar APC ta gudanar da gangami a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, domin nuna goyon baya ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu.
Dubban mutane ne suka halarci gangamin domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu saboda ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a watan Janairun 2027.

Source: Facebook
An yi gangamin goyon bayan Tinubu, Shettima
Ƙungiyar North Central Grassroots Mobilisation Network ce ta shirya gangamin, wanda Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya karɓi baƙuncinsa a filin taro na Lafia Square ranar Asabar, cewar TVC News.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ne ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) zuwa taron, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, gwamnonin Ƙungiyar Gwamnonin APC (PGF), da sauran shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki.
Jam’iyyar ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, 10 ga Oktoba.
Sanarwar ta ce:
“A yau, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyarmu zuwa babban gangamin North Central Grassroots Mobilisation Network, wanda Mai Girma Injiniya Abdullahi Sule, Gwamnan jihar Nasarawa, ya karɓi baƙuncinsa a Lafia Square, jihar Nasarawa.”

Source: Facebook
Musabbabin shirya gangamin da aka yi
Jam’iyyar ta bayyana cewa an shirya gangamin ne domin nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu a watan Janairun 2027, cewar Punch.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“An shirya gangamin ne domin nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Janairun 2027.
Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, gwamnonin Ƙungiyar Gwamnonin APC (PGF), da sauran shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki.”
Haka kuma, jam'iyyar APC ta bayyana cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta halarci gangamin tare da wata tawagar mata daga jihohi shida na yankin siyasar Arewa ta Tsakiya.
Jam’iyyar ta ce:
“Mai Girma Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ita ma ta jagoranci wata tawaga mai ƙarfi ta mata daga jihohi shida na yankin siyasar Arewa ta Tsakiya zuwa gangamin."
Masoyan APC sun yi hatsarin mota
Mun ba ku labarin cewa wasu magoya bayan APC sun yi hatsarin mota a Lafia, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa babban gangamin Tinubu.
Hadarin ya faru ne a ranar Asabar bayan motar bas ɗin da ke ɗauke da magoya bayan ta yi karo da wata mota mai zuwa.
Daniel Ihomun ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce babu wanda ya mutu, amma an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng

