Alaƙa Ta Fara Tsami, Tinubu Ya Samu Hanyar Daƙile Ƙarfin Gwamnoni a Zaɓe
- Rikicin siyasa tsakanin Shugaba Bola Tinubu da wasu gwamnonin APC a Arewa ya tsananta, yayin da ake zargin sun ƙi nuna goyon baya
- Kwamitin gudanarwar APC na ƙasa ya umurci ƴan takara su kai sunayen wakilan jam’iyya kai tsaye hedikwata, domin hana yiwuwar zagon ƙasa
- Wasu gwamnonin Arewa na nuna rashin jin daɗi kan yadda Tinubu ke tafiyar da al’amura, musamman kuɗaɗen ƙananan hukumomi da goyon bayan Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kwamitin gudanarwar APC na ƙasa ya ɗauki matakin dakile zagon ƙasa, ya tsallake gwamnonin wajen zaɓen wakilan jam’iyya.
Rikicin siyasa tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar APC ya ƙara tsananta, sakamakon yadda wasu gwamnonin Arewa suka nuna halin ko-in-kula game da shirin sake zaɓen shugaban ƙasar.

Source: Facebook
Abin da APC ta shirya yiwa gwamnoni
Haka kuma, wasu alamu sun nuna cewa Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na APC ya tsallake gwamnonin, inda ya umarci ƴan takarar jam’iyyar su miƙa sunayen wakilan da suke son amfani da su kai tsaye ga sakatariyar ƙasa, cewar Guardian.
An ɗauki matakin ne domin hana yiwuwar zagon ƙasa yayin babban zaɓen shekarar 2027.
Bayan dawowarsa daga hutun da ya yi a ƙasashen waje kwanan nan, Shugaba Tinubu ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda gwamnonin jihohi ba sa ƙoƙarin wayar da kan al’ummarsu game da nasarorin gwamnatinsa.
Amma shugaban ƙungiyar gwamnoni ya dage cewa al’ada ce a miƙa shugabancin ga gwamnan da yake wa’adi na biyu bayan babban zaɓe.”
Gwamnan ya ce akwai manyan dalilai uku da suka jawo rarrabuwar kawunan wasu abokan aikinsa a Arewa.
APC ta tsallake gwamnonin wajen zaɓen wakilai
Binciken Tribune ya nuna cewa matakin da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na APC ya ɗauka an tsara shi ne domin tabbatar da tsaron nasarar zaɓen jam’iyyar, ta hanyar tsallake rassan jam’iyyar na jihohi waɗanda aka saba miƙa irin waɗannan sunaye ta hannunsu.
Umarnin ya sauya tsarin da jam’iyyar ta saba bi, kuma ana ganin matakin na cikin dabarun hana zagon ƙasa a ranar zaɓe daga gwamnonin da ake zargin suna aiki da wasu manufofi da suka saɓa wa muradun APC.
Majiyoyi da dama a cikin shugabancin jam’iyyar sun tabbatar da cewa an ɗauki matakin ne bayan samun bayanan sirri da ke zargin wasu gwamnonin jihohi da shirya sanya magoya bayansu a matsayin wakilan APC a rumfunan zaɓe, yayin da suke ɗaukar nauyin ƴan takara a jam’iyyun adawa.
A cewar majiyoyin, ana aiwatar da wannan tsari ne musamman a jihohin da kwamitin gudanarwar APC na ƙasa ke zargin gwamnoninsu da ɗaukar nauyin ƴan takarar wasu jam’iyyun siyasa domin fafatawa da ƴan takarar APC a zaɓen 2027.
Wannan mataki ya biyo bayan zargin da wata ƙungiya a Kudu maso Yamma mai suna Oodua Progressive Youths League ta yi cewa wasu gwamnonin da ƴan takarar da suke so suka sha kaye a zaɓen fidda gwani na Majalisar Tarayya sun umurce su da neman tikitin jam’iyyun adawa domin fafatawa da ƴan takarar APC.
A wata sanarwa da Babban Sakataren ƙungiyar, Wale Abdulwaheed, ya sanya wa hannu, ya ce ana zargin gwamnonin sun kuma cimma yarjejeniya da wasu jam’iyyun adawa kan zaɓen wakilan rumfunan zaɓe.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnonin na shirin miƙa sunayen amintattun mutanensu, waɗanda har yanzu mambobin APC ne, domin a amince da su a matsayin wakilan jam’iyyar mai mulki a jihohinsu.
Wani ɗan Majalisar Tarayya daga Ondo, wanda kuma ɗan takarar APC ne a zaɓen 2027, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya nemi a sakaya sunansa saboda yadda batun yake da muhimmanci.
Ya bayyana cewa kwamitin gudanarwar APC na ƙasa ya tsallake Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, inda ya umurci ƴan takara su miƙa sunayen wakilansu kai tsaye ga sakatariyar ƙasa.
Ya ce tuni aka bai wa ƴan takarar fom ɗin da za su cike domin gabatar da sunayen wakilan.
APC ta yi alfahari kan tazarcen Tinubu
An ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta sake jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ne zai samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban Jam’iyyar, Nentawe Yilwatda, ya ce binciken cikin gida da alƙaluman da suka tara sun nuna cewa Tinubu yana gaba da kowa.
Yilwatda ya ayyana cewa APC ba ta tsoron 'yan adawa saboda rashin nasarar da jam'iyyun ADC da NDC suke samu yana ba APC babbar dama.
Asali: Legit.ng


