Makinde Ya Sanar da 'Yan Najeriya Abin da Zai Iya ba Tinubu Matsala a 2027
- Gwamnan Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya bukaci ’yan Najeriya su sauke Bola Tinubu daga mulki a zaɓen 2027
- Makinde ya tunatar da ’yan Najeriya alkawarin Tinubu na magance matsalar wutar lantarki cikin shekaru huɗu
- Jigon APM na ƙasa, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, ya bayyana jam’iyyar a matsayin dandalin siyasa da zai iya magance ƙalubalen ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Alliance People’s Movement (APM), Seyi Makinde, ya ba 'yan Najeriya shawara kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Makinde ya buƙaci ’yan Najeriya su riƙa yi wa Shugaba Bola Tinubu hisabi kan alkawuran da ya ɗauka, sannan su ƙi zaɓensa a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Makinde ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoban 2026 a Yola babban birnin jihar Adamawa, yayin taron tattaunawa da al’ummar Arewa maso Gabas na jam’iyyar APM, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar da ’yan takararta sun tsara dabarun tunkarar babban zaɓen 2027 a yayin taron.
Makinde ya tuna wa Tinubu alkawarin wutar lantarki
Da yake jawabi a wajen taron, Makinde ya tuna cewa Tinubu ya yi alkawarin magance matsalolin wutar lantarki a Najeriya cikin shekaru huɗu.
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su yi la’akari da halin da ɓangaren samar da wutar lantarki yake ciki yayin da suke yanke shawarar wanda za su zaɓa a babban zaɓe na gaba.
“Don haka, idan har yanzu ba a magance matsalar wutar lantarki ba, to ku ’yan Najeriya kun san inda za ku kaɗa ƙuri’unku domin samar da kyakkyawar makoma ga matasanmu.” In ji shi
Bala Mohammed ya nemi goyon bayan ’yan Najeriya
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APM na ƙasa kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yaba wa mambobi da masu ruwa da tsaki kan goyon baya da haɗin kan da suka nuna wajen tarbar Makinde a yankin Arewa maso Gabas.
Bala Mohammed ya bayyana APM a matsayin sahihin dandalin siyasa da zai iya magance ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su ba jam’iyyar da ’yan takararta goyon baya a babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Makinde ya cika baki kan zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na shirin lashe zaben 2027 da gagarumin rinjaye.
Makinde ya ce APM na da burin samun aƙalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103 (kimamin kuri'u miliyan 68) da suka yi rajista domin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.
Ya ce yaƙin neman zaɓen ya mayar da hankali ne kan “Sake Gina Najeriya”, yana mai bayyana hakan a matsayin mafita ɗaya tilo da za ta iya magance ƙalubalen ƙasar da gyara abubuwan da ba sa aiki yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng

