Zabe Ya Wuce, Trump na Shirin Kaddamar da Manyan Hare Hare Iran

Zabe Ya Wuce, Trump na Shirin Kaddamar da Manyan Hare Hare Iran

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gana da jami’an tsaron ƙasarsa domin tattauna yiwuwar sake fara hare-haren soji kan Iran
  • Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Amurka ta fara kammala shirye-shiryen yiwuwar sake kai manyan hare-hare Tehran
  • Iran ta miƙa wa Amurka wani sabon shirin tattaunawa kan makamashin nukiliya ta hannun Qatar, yayin da Rasha ke ƙoƙarin ƙarfafa tattaunawar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gana da tawagar jami’an tsaron ƙasarsa ranar Alhamis domin tattauna yiwuwar sake fara yaƙi da Iran.

Jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa an gudanar da tarurruka a fadar White House a ranakun Laraba da Alhamis domin duba matakin da ya kamata a ɗauka kan rikicin.

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump ke jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Fox News ta rahoto cewa ranar 9 ga Nuwamba sabon watan Hijira zai kama a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ke nufin ƙarancin hasken wata a daren. Jami’an sun ce irin wannan yanayi na iya sauƙaƙa gudanar da ayyukan soji.

Kara karanta wannan

Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano

Trump na shirin kai hari Iran

Da yake magana da manema labarai a ofishinsa na fadar White House ranar Alhamis, Trump ya ce gwamnatinsa za ta yanke shawara kan ko za ta sake kai hare-hare kan Iran.

Ya bayyana cewa Amurka na nazarin ko za ta ƙara kai hare-hare domin tabbatar da cewa an lalata shirin nukiliyar Iran har abada.

Trump ya ce ba ya son lalata sauran sassan ƙasar Iran idan akwai wata hanyar kauce wa hakan, amma ya yi gargaɗin cewa yana iya zama dole a ɗauki irin wannan mataki.

Shugaban ya kuma ce nan ba da daɗewa ba jama’a za su san matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka.

Sojojin Amurka na shiri

Rahotanni da suka ambato wani jami’in Amurka sun bayyana cewa rundunar sojin ƙasar da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, na kammala shirye-shiryen yiwuwar sake fara manyan hare-hare kan Iran.

Kara karanta wannan

Shin tallafin N50,000 da aka fara turawa 'yan Najeriya bashi ne ko kyauta? An samu bayani

Sai dai rundunar ba ta samu sabon umarni daga gwamnatin Amurka na fara kai hare-haren ba.

A wani ɓangare na rikicin, Firaministan Iraqi, Ali Faleh Al-Zaidi, ya tattauna da Trump ta wayar tarho ranar Alhamis, inda ya jaddada cewa bai kamata a yi amfani da ƙasar Iraqi wajen kai hare-hare kan ƙasashen maƙwabta ba.

Jagoran kasar Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei da ke jagorantar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta miƙa wa Amurka sharuda

A wani ɓangare na ƙoƙarin diflomasiyya, rahotanni sun bayyana cewa Iran ta miƙa wa Amurka wani sabon shiri kan batun makamashin nukiliyarta ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar.

Amurka na nazarin shirin, yayin da Iran ke jiran a cika wasu buƙatu guda bakwai da ta gabatar domin cimma matsaya.

Al Jazeera ta rahoto cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya gana da babban jami’in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, a birnin Moscow ranar Alhamis domin tattauna batutuwan tsaro da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya yi gargaɗin tsige shi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargaɗin cewa yunƙurin da jam’iyyar Democrat za ta yi na tsige shi daga mulki zai jawo mata babbar asara a siyasa.

Kara karanta wannan

Indonesia: An yi wa shugaban kasa kutse a waya, an saurari maganganun da yake yi

Trump ya bayyana hakan ne bayan jam’iyyar Republican ta sha kaye a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki, inda Democrat suka samu rinjaye a majalisa.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana fatan cewa nasarar Democrat za ta ƙara wa ƙasarsa damar samun tallafin Amurka a yaƙin da take yi da Rasha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng