Kano: Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Kisan Fatima da Yayanta 6

Kano: Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Kisan Fatima da Yayanta 6

  • Babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Umar Auwalu mai shekara 23 da Yakubu Daiyebu mai shekara 21 hukunci
  • An samu mutanen biyu da laifin kashe Fatima Abubakar mai shekara 35 da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi ranar 17 ga Janairu, 2026
  • Kotun ta kuma yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai tare da aikin wahala bisa laifuffukan haɗa baki da fashi da makami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wata babbar kotun jihar Kano da ke zaune a ɗakin shari’a na 11 ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin kashe wata matar aure mai shekara 35, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida.

An kashe Fatima da ’ya’yanta ne a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano, ranar 17 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake ta'addanci, an kashe mutane da sace bayin Allah a Kaduna

Kotu ta yanke hukunci a shari'ar kisan Fatima
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Umar Auwalu, mai shekara 23, mazaunin unguwar Sabuwar Gandu, da Yakubu Daiyebu, mai shekara 21, daga Sabon Gida da ke unguwar Sharada, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kotun ta kuma yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai tare da aikin wahala bisa laifuffukan haɗa baki domin aikata kisan kai da kuma fashi da makami.

Alƙali ya yi magana kan kisan

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Nasiru Saminu ya bayyana kisan a matsayin ɗaya daga cikin munanan laifuffukan da suka fi tayar da hankali a tarihin shari’ar manyan laifuffuka.

Alƙalin ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda waɗanda suka aikata kisan ’yan uwa ne da ya kamata su kasance masu kare waɗanda aka kashe.

Ya bayyana cewa matar ta buɗe wa wanda ake tuhuma na farko ƙofa da kanta lokacin da ya zo tare da abokin aikinsa, ba tare da sanin cewa suna da niyyar kai wa iyalinta hari ba.

Kara karanta wannan

Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano

A cewarsa, waɗanda aka samu da laifin sun yi amfani da amincewar da marigayiyar ta yi da su kafin su kai harin da ya hallaka dukkan iyalinta.

Mai shari’a Saminu ya ce Fatima ba wai kawai mutum ce da aka kashe ba, har ila yau uwa ce wadda rayuwarta ke da alaƙa da fata, jin daɗi da makomar ’ya’yanta.

“An rasa rayuka bakwai. An kawo ƙarshen makomar mutane bakwai. An kuma katse damar mutane bakwai ta rayuwa, cimma burinsu da bayar da gudummawa ga al’umma har abada.” In ji shi.

Kotun ta jajanta wa mijin marigayiyar

Alƙalin ya kuma nuna tausayawarsa ga ’yan uwan waɗanda aka kashe da suka tsira, musamman Haruna Bashir, mijin Fatima kuma mahaifin yaran shida.

Ya ce lamarin ya jefa Bashir cikin matsanancin baƙin ciki, yanke ƙauna da raɗaɗin da ya shafi tunaninsa.

Mai shari’a Saminu ya bayyana cewa babu wani hukuncin kotu da zai iya dawo da waɗanda aka kashe ko kuma ya biya iyalinsu diyyar irin wannan babban rashi.

Sai dai ya jaddada cewa aikin kotu shi ne tabbatar da adalci, ba ɗaukar fansa ba, don haka dole ne ta yanke hukunci bisa doka da hujjojin da aka gabatar mata.

Kara karanta wannan

Ta'addancin 'yan bindiga ya ritsa da sojoji da mai juna biyu a Taraba

An ambaci Alƙur’ani kafin yanke hukuncin

A yayin yanke hukuncin, alƙalin ya ambaci aya ta 45 a cikin suratul Ma’ida da ke magana kan ƙa’idar ɗaukar rai bisa rai.

Kotun ta samu mutanen biyu da laifin kisan kai da hukuncinsa shi ne kisa, ƙarƙashin sashe na 221 na dokar Penal Code.

Baya ga hukuncin kisa, an yanke musu ɗaurin rai da rai tare da aikin wahala bisa laifuffukan haɗa baki da fashi da makami.

A gefe guda kuma, an sallami mutum na uku da ake tuhuma, Isyaku Yakubu, mai shekara 40, tare da wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wanda ake tuhuma na farko ya roƙi kotu ta yi masa sassauci bayan amincewa da laifinsa, yayin da na biyu ya musanta aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng