Ana Wata ga Wata: Shettima Ya Yi Wa Atiku Shagube a Wurin Kamfen
- Shugaba Bola Tinubu ya ce abokan hamayyarsa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu ba su da ƙwarewar siyasa da shugabanci irin na sa
- Tinubu ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da alkawuran da ta ɗauka a zaɓen 2023, kuma yana neman wa’adi na biyu domin ƙarfafa nasarorin farko.
- Ya nemi al’ummar jihar Ekiti su ba shi aƙalla kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce abokan hamayyarsa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu ba su da ƙwarewar siyasa da shugabanci da za su iya kaiwa matsayin gogewarsa.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma alkawuran da ta ɗauka wa ’yan Najeriya a zaɓen 2023, tun bayan hawanta mulki.

Source: Facebook
Ya ce burinsa na neman wa’adi na biyu shi ne tabbatar da dorewar ayyukan raya ƙasa da sauran nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta samu a wa’adin farko, cewar rahoton jaridar The Punch.
Tinubu ya nemi 90% na ƙuri’un Ekiti
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Tinubu a wajen wani gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da kwamitin APC Presidential Campaign Council ta shirya a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026.
An gudanar da taron ne a Ekiti Parapo Pavilion da ke birnin Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti. A yayin jawabin, Tinubu ya roƙi masu zaɓe a jihar da su ba shi aƙalla kashi 90 cikin 100 na jimillar ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Ya ce samun wannan gagarumin goyon baya zai ba shi damar ci gaba da riƙe muƙaminsa da kuma aiwatar da shirye-shiryen raya ƙasar.
Abin da Shettima ya ce kan Atiku
A wani ɓangare na jawabin, mataimakin shugaban ƙasar ya mayar da hankali kan abokan hamayyarsa, musamman ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar.
Shettima ya yi amfani da jihar Adamawa a matsayin misali, inda ya ce tun bayan komawa mulkin dimokuraɗiyya a 1999, jihar ta samu gwamnoni biyar, amma babu ɗaya daga cikinsu da ke tare da Atiku.
Ya tambayi ko Gwamna Umaru Fintiri na goyon bayan Atiku, sannan ya ambaci tsofaffin gwamnoni Boni Haruna, Bala Ngilari, Murtala Nyako da Bindow Jibrilla.
Shettima ya ce babu ɗaya daga cikin waɗannan tsoffin gwamnoni da ke tare da Atiku, yana mai cewa dukkaninsu na goyon bayan takararsa, TheCable ta kawo labarin.
Tambayar da ya yi wa Atiku
Mataimakin shugaban ƙasar ya yi tambaya kan yadda Atiku zai samu tasiri a sauran jihohin Najeriya idan har bai samu goyon bayan manyan ’yan siyasa a jiharsa ta asali ba.
“Idan ba za ka iya tafiyar da al’amuran jiharka ba, idan ba ka da tasiri a jiharka, ta yaya za ka zama mai tasiri a wasu wurare?” In ji shi.
Shettima ya ƙara da cewa siyasa abu ne na yawan ƙuri’u, sannan ya tambayi irin saƙon da Atiku zai isar wa masu zaɓe a jihohin Osun, Ogun, Kaduna, Legas da Ribas, da sauran sassan ƙasar, idan ba shi da tasiri a gida.

Source: Facebook
Shettima ya nemi a zabi Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya mika bukatarsa ga masu zabe a yankin Arewacin Najeriya.
Shettima ya buƙaci masu zaɓe a yankin Arewa su haɗa kai wajen mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Asali: Legit.ng


