Magana Ta Kare, ADC Ta Daukaka Kara kan Hukuncin da Ya Soke Takarar Atiku a Zaben 2027

Magana Ta Kare, ADC Ta Daukaka Kara kan Hukuncin da Ya Soke Takarar Atiku a Zaben 2027

  • Jam’iyyar ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na ranar 5 ga Nuwamba, 2026, a shari’ar da Nafiu Bala Gombe ya shigar
  • ADC ta kuma nemi kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an saurari ƙarar da ta ɗaukaka
  • Jam’iyyar ta sanar da INEC matakan da ta ɗauka, tare da kira ga mambobinta da magoya bayanta su kwantar da hankalinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1619/2025.

Hon. Nafiu Bala Gombe shi ne ya shigar da karar, inda daga karshe kotu ta rusa shugabancin ADC karkashin tsohon shugaban Majalisar dattawa, Sanata David Mark.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya yi maganganu kan rusa takarar Atiku

David mark.
Tsohon shugaban Majalisar dattawa kuma shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark Hoto: David Mark
Source: Twitter

Jam'iyyar ADC ta daukaka kara

Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta kuma shigar da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai kotun ɗaukaka ƙara ta saurari ƙarar tare da yanke hukunci a kanta.

ADC ta ce ta sanar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a hukumance game da waɗannan matakai a ranar 6 ga Nuwamba, inda ta buƙaci ta dakatar da ɗaukar wasu matakai kan batun yayin da ake jiran hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa, Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC.

ADC ta aika sako ga hukumar INEC

Ya ce bai kamata INEC ta ɗauki wani mataki da zai shafi shari’ar ba, kasancewar har yanzu kotu ba ta yanke hukunci kan buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin ba.

Sanarwar ta ce:

“Har yanzu ba a yanke hukunci kan buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin ba. Don haka, dole ne INEC ta yi taka-tsantsan.

Kara karanta wannan

2027: Kotu ta rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

"Kada ta yi kamar babu ƙarar da aka ɗaukaka da kuma buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin, ko kuma ta ɗauki matakin da zai riga kotun ɗaukaka ƙara yanke hukunci, tare da kawo cikas ga warware wannan batu yadda ya kamata.
"Dole ne hukumar ta mutunta tsarin shari’a ta ba kotun ɗaukaka ƙara damar sauraron ƙarar.”
Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar a wurin taron hadakar yan adawa Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Shaibu ya ƙara da cewa ADC tana amfani da haƙƙinta na doka na ɗaukaka ƙara, don haka ya kamata a bar tsarin shari’a ya ci gaba har zuwa ƙarshe.

Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar, magoya bayanta da ’yan Najeriya masu goyon bayan dimokuraɗiyya da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu haƙuri da kwarin gwiwa.

INEC ta yi bayani kan takarar Atiku

Kun ji cewa hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta ce har yanzu ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun da ya kori shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark ba.

INEC ta musanta rahotannin da ke cewa ta cire sunayen Atiku Abubakar da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, daga shafinta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262