Abin da Ƴan Kwankwasiyya Suka Ce da Kotu Ta Rushe Takarar Su Atiku

Abin da Ƴan Kwankwasiyya Suka Ce da Kotu Ta Rushe Takarar Su Atiku

  • Ƙungiyar Kwankwasiyya ta nuna damuwa kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke shugabancin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC
  • Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa yawan shari’o’in shugabancin jam’iyyun adawa na iya raunana dimokuraɗiyya da hana su shirin zaɓen 2027
  • Kwankwasiyya ta buƙaci INEC da bangaren shari’a su kasance masu adalci, tare da tabbatar da babu nuna fifiko ga wani ɓangaren siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Ƙungiyar Kwankwasiyya ta nuna matuƙar damuwa kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta yanke ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2026.

Hukuncin ne ya soke shugabancin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark da matakan da aka ɗauka a ƙarƙashinsa.

Kwankwasiyya ta yi magana bayan hana Atiku takara
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya sanya wa hannu, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Zaɓi 2 da suka rage wa Atiku bayan rushe takararsa, shugabannin ADC

Kwankwasiyya ta ce duk da amincewarta da ikon kundin tsarin mulki da bangaren shari’a ke da shi na warware rikice-rikice, tana fargabar yadda ake yawan kai batutuwan shugabancin jam’iyyun adawa da zaɓen ’yan takara gaban kotu.

Ta bayyana cewa irin waɗannan shari’o’i na raunana damar jam’iyyun adawa wajen tsara ayyukansu da kuma shirye-shiryen tunkarar zaɓe.

Kwankwasiyya ta damu da makomar dimokuraɗiyya

Ƙungiyar ta ce dole ne a gina dimokuraɗiyyar Najeriya bisa tsarin siyasa mai bai wa kowa dama, ’yancin hukumomi, da daidaito a gaban doka.

Ta kuma jaddada muhimmancin kare haƙƙin ’yan kasa na shiga ƙungiyoyin siyasa da kuma bayar da gudummawa a harkokin zaɓe.

Kwankwasiyya ta yi gargaɗin cewa tsawaita rikice-rikicen shugabanci da bambancin fahimtar dokoki a kotuna, a lokacin da ya kamata jam’iyyun siyasa su ƙarfafa tsarinsu domin tunkarar zaɓe cikin gaskiya, na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

Haka kuma, ta ce hakan na iya takaita damar gudanar da harkokin dimokuraɗiyya cikin ’yanci.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya yi maganganu kan rusa takarar Atiku

Kwankwasiyya ta yi gargaɗi kan rusa takarar Atiku
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

An buƙaci bangaren shari’a ya yi adalci

Ƙungiyar ta yi kira ga bangaren shari’a da ya gudanar da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa bisa cikakken ’yanci, rashin nuna son kai, gaskiya da kuma bin ƙa’idojin aiki.

Ta jaddada cewa dukkan ɓangarorin da ke cikin takaddamar siyasa suna da haƙƙin samun adalci da sauraron ƙararrakinsu.

Ta kuma buƙaci duk wani hukunci da kotu za ta yanke ya kasance bisa doka, hujjojin da aka gabatar da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulki da sauran dokokin ƙasa, ba tare da la’akari da wasu abubuwan da ba su da alaƙa da shari’ar ba.

An gargadi gwamnatin tarayya da INEC

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta nuna a aikace cewa tana goyon bayan tsarin siyasa mai bai wa kowa dama.

Ta ce ya kamata gwamnati da hukumomin da ke ƙarƙashinta su guji amincewa ko cin moriyar duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga halastattun ayyukan jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Obi ya shiga wa Atiku fada kan rusa 'yan takarar ADC da kotu ta yi

Kwankwasiyya ta ce dole ne INEC ta tabbatar da cewa babu wani ɓangaren siyasa da ake bai wa fifiko wajen gudanar da ayyukan hukumar.

ADC ta magantu bayan hukuncin kotu

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar ADC ta yi martani bayan babbar kotun tarayya ta soke shugabancinta da takarar Atiku Abubakar.

Jam’iyyar ta yi watsi da hukuncin kotun tare da bayyana cewa za ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

ADC ta kuma yi barazanar kai korafi ga majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa kan yadda aka gudanar da shari’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.