2027: Arewa Ta Shirya Gagarumin Gangamin Tallata Tinubu da Shettima
- Jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiya ta shirya gudanar da gagarumin gangami a Lafia domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu
- Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce za a tattara magoya baya daga jihohi shida da Abuja
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, zai halarci taron da uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya ta sanar da shirin gudanar da gagarumin gangami a Lafia, babban birnin Nasarawa.
Za a yi gangamin ne domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima gabanin zaɓen 2027.

Source: Facebook
An shirya gangamin ne ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar North Central Grassroots Mobilisation Network, cewar Vanguard.
Gwamnan da zai karbi bakuncin taron
Yayain da Gwamnan Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, zai karɓi baƙuncin taron, ana kuma sa ran uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta jagoranci taron.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, bayan wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Abuja.
Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, gwamnonin yankin da mataimakansu, ministoci, ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa.

Source: Facebook
Alkawarin da aka yi wa Tinubu
Yilwatda ya ce mahalarta taron sun amince su tattara tsarin siyasa da magoya bayansu a faɗin jihohi shida na Arewa ta Tsakiya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin halartar gangamin Lafia.
Ya bayyana gangamin da ake shirin gudanarwa a matsayin “uwar dukkan gangamomi”, yana mai cewa zai nuna irin goyon bayan da yankin ke bai wa tikitin Tinubu da Shettima gabanin zaɓen 2027.
A cewarsa, taron ya kuma tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai da daidaita ayyukan shugabannin jam’iyyar da ƙungiyoyin magoya baya a matakin ƙasa domin tabbatar da ingantaccen tattara jama’a.
Ya ce mahalarta taron sun amince da rawar da Akume ya taka wajen haɗa kan shugabannin siyasa daga Arewa ta Tsakiya. Sun kuma yaba wa Gwamna Sule bisa amincewa da karɓar baƙuncin gangamin a Nasarawa.
Masu ruwa da tsakin sun kuma duba shirye-shiryen halartar shugabannin jam’iyya, mata, matasa, ƙungiyoyin al’umma da magoya baya daga sassa daban-daban na yankin, tare da sake tabbatar da aniyarsu ta ganin an gudanar da gangamin cikin nasara.
Masoyin Atiku ya koma tafiyar Tinubu
An ji cewa wani fitaccen amfani da kafafen sada zumunta a Arewa Al’ameen Yabo, ya sauya goyon bayansa daga Atiku Abubakar zuwa Bola Tinubu a 2027.
Yabo ya nemi afuwar Tinubu kan zaɓen Atiku da ya yi a 2023, yana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da NELFUND sun canza ra’ayinsa.
Wasu ’yan Najeriya sun goyi bayan matakin Yabo, yayin da wasu suka soki ra’ayinsa, suna danganta gwamnatin Tinubu da tsadar rayuwa da matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng

