Zance Ya Kare: Atiku Ya Bayyana Makomar Takararsa a 2027 bayan Hukuncin Kotu
- Atiku Abubakar ya buƙaci magoya bayansa su ci gaba da jajircewa, yana mai cewa har yanzu yana cikin tseren neman shugabancin Najeriya a 2027
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da rushe duk matakan da shugabancin ya ɗauka
- Atiku ya zargi gwamnatin APC da amfani da matsin lamba da dabarun kotu wajen raunana jam’iyyun adawa, yana mai cewa ba zai janye daga takara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja -Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci magoya bayansa da su ci gaba da jajircewa, yana mai tabbatar musu cewa har yanzu yana cikin tseren neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027.
A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da rushe duk matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaman Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Source: Facebook
Atiku ya tabbatar da cewa yana cikin takara
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamban 2026, tohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce har yanzu yana cikin takarar shugaban ƙasa kuma ba shi da niyyar ficewa.
Sai dai Atiku ya ce hukuncin ba zai sa ya janye daga takarar ba, inda ya ci gaba da harkokin yaƙin neman zaɓensa duk da matakin kotun.
"Ina cikin wannan takara. Ba zan je ko’ina ba. Za a saka sunana cikin takardar zaɓe. Babu barazana, baƙar magana ko amfani da dabarun kotu da zai sa na yi watsi da ku ko manufar da muke tare da ita.” In ji shi.
Atiku ya yi zargin cewa sabon hukuncin kotun bai nuna muradin al’ummar Najeriya ba.
“Babu wani maguɗi, hasashe ko ƙirƙirar labari da zai iya goge matsayinmu a wannan takara, rufe bakin yaƙin neman zaɓenmu ko hana ’yan Najeriya ’yancin zaɓar makomarsu. Muna cikin takara, kuma dole ne a bar al’umma su yanke hukunci.” In ji shi.
Ya zargi APC da raunana jam’iyyun adawa
Atiku ya yi suka ga jam’iyya mai mulki, ba tare da ambaton sunanta kai tsaye ba, inda ya ce mutanen da ke ikirarin suna da gwamnoni 32, tare da zargin saye ko matsa wa shugabannin wasu jam’iyyu lamba su koma cikinsu, bai kamata su ji tsoron sahihin zaɓe ba.
Ya ce maimakon su gabatar da ayyukan da suka yi wa ’yan Najeriya, masu mulki na amfani da dabaru daban-daban domin raunana jam’iyyun adawa.
Daga cikin abubuwan da ya lissafa akwai matsin lambar siyasa, ƙirƙirar labarai, amfani da dabarun shari’a da kuma yunƙurin yin maguɗi a rajistar masu zaɓe ta hanyar amfani da hotunan da aka ƙirƙira da basirar na’ura (AI), sunayen ƙarya da mutanen da babu su.
Atiku ya ce irin waɗannan matakai ba ayyukan mutanen da suka gamsu da nasarorin da suka samu ba ne, a cewarsa, yunƙuri ne na hana sahihiyar hamayya da kuma tura Najeriya zuwa tsarin mulkin jam’iyya ɗaya.

Kara karanta wannan
"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027
Atiku ya soki manufofin gwamnatin Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma zargi gwamnatin yanzu da rashin samun nasarorin da za ta iya karewa a gaban ’yan Najeriya. Ya ce gwamnatin ta cire tallafin man fetur cikin dare ɗaya ba tare da tanadin da zai kare jama’a daga illolin matakin ba.
Atiku ya kuma zargi gwamnatin da gazawa wajen dakile faɗuwar darajar Naira da kuma tsadar abinci, wanda ya ce ya wuce ƙarfin talakawa.
Atiku ya ƙara da cewa masana’antu da ƙananan sana’o’i sun rufe, matasa na barin ƙasar domin neman kyakkyawar makoma, yayin da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke ci gaba da addabar al’ummomi.
Ya buƙaci magoya bayansa kada su karaya, yana mai cewa ƙuri’unsu ne ƙarfin da suke da shi wajen sauya shugabancin ƙasar.
Ya yi kira da a kare dimokuraɗiyya
Atiku ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen hana yunƙurin mayar da Najeriya ƙasar da jam’iyya ɗaya ce kawai ke da iko.

Kara karanta wannan
Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya
Ya jaddada cewa Najeriya ta kowa ce, kuma dimokuraɗiyyarta ya kamata ta kasance a buɗe ga jam’iyyu da ra’ayoyi daban-daban.
Ya ƙalubalanci masu mulki da su je zaɓe idan sun amince da yawan magoya bayansu da ayyukan da suka yi.
A ƙarshe, Atiku ya ce:
“Bari na bayyana wannan a sarari: Bola ba zai iya amfani da kotuna ya kuɓuta daga hukuncin da ’yan Najeriya za su yanke masa a akwatin zaɓe ba.”

Source: Facebook
APC da Tinubu na fargabar Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba da shawara kan harkokin shari’a na ADC, Oserheimen Osunbor, ya zargi jam’iyyar APC da fargabar fuskantar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jigon na ADC ya ce alamu sun nuna APC tana tsoron dan takararta na shugaban kasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara da dan takara mai karfi kamar Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng

