Jita Jita Ta Kare, INEC Ta Yi Magana kan Takarar Atiku bayan Hukuncin Kotu
- Hukumar zaɓe ta ƙasa ta ce har yanzu ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun da ya kori shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark ba
- INEC ta musanta rahotannin da ke cewa ta cire sunayen Atiku Abubakar da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, daga shafinta
- Hukumar ta ce ba ta tattauna batun hukuncin ba, yayin da ADC da Atiku suka yi watsi da shi tare da shirin ɗaukaka ƙara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun tarayya da ya kori shugabancin jam’iyyar ADC) ƙarƙashin jagorancin David Mark ba.
Hukumar INEC ta bayyana har yanzu ba ta karbi kwafin hukuncin kotun ba, wanda ya soke tikitin duka yan takarar ADC ciki har da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Source: Facebook
Da gaske INEC ta cire sunan Atiku?
Daily Trust ta rahoto cewa bayan hukuncin, wasu rahotanni sun fara yaɗuwa a kafafen sada zumunta cewa INEC ta cire sunan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, daga shafinta na intanet.
Sai dai Malam Mohammed Kudu Haruna, kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe (IVEC), ya ce hukumar ba ta karɓi kwafin hukuncin ba, kuma ba ta tattauna batun ba.
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar a shafin hukumar INEC a ranar Juma’a ya nuna cewa har yanzu sunayen ’yan takarar na nan, sabanin abin da ake yaɗawa a intanet.
Haruna ya nuna shakku kan inda aka samo bayanin, yana mai jaddada cewa hukumar ba ta karɓi hukuncin kotun ba.
“Ban san daga ina wannan sanarwa ta fito ba. Wani ne kawai ya turo min ita. Har yanzu ba mu karɓi hukuncin ba,” in ji shi.
INEC na dakon kwafin hukuncin kotu
Ya bayyana cewa samun sahihin kwafin hukuncin kotu na ɗaukar lokaci, inda ya ce ba za a yi tsammanin hukumar za ta ɗauki mataki kan hukuncin da ba ta karɓa a hukumance ba.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ba ta yi zama domin tattauna hukuncin ba, yana mai cewa matsayinta zai ci gaba da kasancewa bisa tsarin shari’a da ake bi.
Wannan bayani na INEC ya zo ne kwana guda bayan da Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke shugabancin ADC ƙarƙashin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.

Source: Facebook
Haka zalika ya soke matakan da shugabancin David Mark ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen 2027.
INEC ta ce har yanzu ba a mika mata hukuncin kotun ba, don haka ba za ta dauki wani mataki a ba har sai ta karbi kwafin a hukumance.
Jam'iyyu 9 sun goyi bayana ADC
Kun ji cewa jam’iyyun adawa tara karkashin kungiyar Coalition for Democracy sun nuna goyon bayansu ga jam’iyyar adawa ta ADC.
Jam'iyyun siyasa 9 sun bayyana hukuncin kotun da ya rushe shugabancin David Mark a ADC a matsayin barazana ga dimokuradiyya
Asali: Legit.ng


