Zaben 2027: NDC Ta Dauko da Zafi, Ta Fallasa Makarkashiyar da APC Ke Shirya Mata

Zaben 2027: NDC Ta Dauko da Zafi, Ta Fallasa Makarkashiyar da APC Ke Shirya Mata

  • NDC ta zargi APC da matsa wa wasu otal-otal a Abuja lamba domin su ƙi bai wa jam’iyyar damar amfani da wuraren taronsu
  • Sakataren yaɗa labaran NDC na ƙasa, Osa Director, ya ce Rockview Hotel ya soke yarjejeniyar amfani da wurinsa sau biyu
  • Jam’iyyar ta kuma zargi BON Hotel da ƙin amincewa da buƙatarta, duk da cewa ta cika dukkan sharuddan da otal ɗin ya gindaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta yi zarge-zarge kan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jam'iyyar NDC ta zargi APC da matsa wa wasu otal-otal a Abuja lamba domin hana jam’iyyar adawa amfani da wurarensu wajen gudanar da taruka.

NDC ta yi zargi kan APC
Jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson na jawabi a wajen taro Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da NDC ta fitar a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026 ta hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Osa Director.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar tsaigaita wuta da Boko Haram

Sakatan yada labaran na NDC ya ce ƙoƙarin takura wa dimokuraɗiyya da kuma hana ’yan adawa bayyana ra’ayoyinsu na ƙaruwa.

Osa Director ya zargi Rockview Hotel da soke yarjejeniyar da ya yi da jam’iyyar domin amfani da wurarensa wajen taro a lokuta biyu, duk da cewa otal ɗin ya fara amincewa da buƙatarsu.

NDC ta zargi Rockview Hotel da soke yarjejeniya

A cewar sanarwar, lamarin farko ya faru ne a watan Yunin 2026, lokacin da otal ɗin ya janye amincewarsa a mintin ƙarshe, inda ya hana jam’iyyar gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na biyu (NEC).

Sanarwar ta ce:

“Ba wai kawai jami’an APC mai mulki sun mayar da NDC abin kai wa hari ba, har ma ta zama abin nuna wariya daga masu otal-otal da harkar masauki a Abuja.”

Director ya ƙara da cewa a wani sabon lamari, Rockview Hotel ya sake hana jam’iyyar amfani da wurarensa domin gudanar da wani taro, inda aka ce an ɗauki matakin ne bisa umarnin wasu daga sama.

Kara karanta wannan

JD Vance: Mataimakin Trump ya fito da ainihin dalilan da suka jawo rashin nasararsu a zabe

“A lokuta biyu, Rockview Hotel da ke Abuja ya amince da amfani da wurarensa domin tarukanmu, amma ba tare da wani sahihin dalili ba, sai ya soke yarjejeniyar a mintin ƙarshe.” In ji shi.

NDC ta zargi BON Hotel da ƙin ba ta wurin taro

Jam’iyyar ta kuma zargi BON Hotel da ke Wuse, Abuja, da ƙin ba ta damar amfani da wurarensa domin gudanar da taro, duk da cewa ta cika dukkan sharuddan da otal ɗin ya gindaya.

A cewar Director, matsalar ta kuma shafi bikin da NDC ta shirya na bayyana mambobin majalisar yaƙin neman zaɓenta ta ƙasa.

Ya ce otal ɗin da aka shirya gudanar da bikin ya nemi a mayar masa da kuɗin da jam’iyyar ta riga ta biya, bayan ya sanar da cewa ba ya son samar da wurin gudanar da taron.

Sai dai ya bayyana cewa daga ƙarshe otal ɗin ya bar jam’iyyar ta gudanar da bikin bayan NDC ta dage cewa za ta yi amfani da wurin da ta riga ta biya kuɗinsa.

NDC ta yi muhimmin kira ga APC

Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce ’yan Najeriya sun cancanci samun shugabanci nagari, yana mai cewa NDC a shirye take ta yi wa ƙasar hidima cikin kishin ƙasa da ƙwazo.

Kara karanta wannan

Yadda masu Opay za su iya karbar tallafin N50,000 duk wata na gwamnatin tarayya

"Wannan ba dimokuraɗiyya ba ce. Ya kamata APC ta bar dukkan jam’iyyun siyasa su gudanar da kamfe ba tare da wani shamaki ko tangarda ba, domin bai wa ’yan Najeriya damar zaɓar waɗanda suke so su shugabance su.” In ji shi.

Haka kuma, ya yi kira ga ’yan Najeriya masu kishin dimokuraɗiyya da sauran masu fatan alheri ga ƙasar da su yi Allah-wadai da abin da ya kira matakan da Rockview da BON Hotel suka ɗauka.

NDC ta yi zargi kan ADC
Peter Obi da Sanata Seriake Dickson a wajen taron NDC Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

An farmaki tawagar Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan daba sun kai hari kan ayarin motocin da ke ɗauke da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Alhaji Rabiu Kwankwaso.

Maharan sun farmaki ayarin Obi da Kwankwaso ne s daidai mahadar Watt Market Roundabout da ke Calabar, babban birnin Jihar Cross River.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng