Sojoji Sun Kwato Waɗanda Ƴan Bindiga Suka Sace, an Samu Miliyoyin Kuɗi, Makami
- Dakarun sojojin Najeriya sun ceto mutane 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su yayin wani samame a jihar Neja
- Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, bama-bamai uku, babura 33, alburusai da kuɗi sama da Naira miliyan 4.7
- Rundunar sojin ta ce ta yi artabu da ’yan ta’addan da suka tsere zuwa daji bayan samun raunukan harbin bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a jihohin Neja da Kebbi.
Har ila yau, sojojin sun kwato makamai da kuɗi sama da Naira miliyan 4.7 a wasu hare-hare kan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a jihar Neja.

Source: Facebook
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kuma kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, bama-bamai uku kirar RPG, babura 33, alburusai da wasu kayayyaki yayin samamen, cewar Punch.
Yadda sojoji suka ceto mutane 16 a Neja
A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji ta 18 Brigade, Kyaftin Adebayo Adewumi, ya sanya wa hannu ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2026, rundunar ta bayyana yadda aka gudanar da samamen.
Sanarwar ta ce samamen farko ya gudana ne ranar 5 ga watan Nuwamba, bayan samun bayanan sirri kan motsin ’yan ta’adda daga ƙaramar hukumar Mashegu zuwa Rijiyan Nagwamatse da ke ƙaramar hukumar Kontagora a jihar.
A yayin artabun, dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan ta’addan, duk da cewa ba a tabbatar da adadinsu ba, sannan suka samu nasarar ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigogi kirar AK-47 guda biyu, harsasai bakwai na bindiga, bama-bamai uku kirar RPG, babura 33 da kuɗi Naira 4,105,000.

Source: Twitter
Sojoji sun fatattaki ’yan ta'adda a Neja
A wani samame makamancin haka da aka gudanar ranar 3 ga watan Nuwamba, sojoji sun tare wasu ’yan ta’adda da ke tafiya daga ƙauyen Makuku a ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi zuwa Tungan Kawo a ƙaramar hukumar Rijau ta jihar Neja.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi musayar wuta mai zafi da ’yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa dajin da ke yankin.
An ce ’yan ta’addan sun tsere ne da raunukan harbin bindiga daban-daban, yayin da sojojin suka gudanar da bincike a yankin bayan artabun.
Binciken ya kai ga kwato babura guda biyar, wayar hannu, kuɗi Naira 644,300 da wasu kayayyaki, cewar rahoton Vanguard.
Sojoji sun musanta yarjejeniya da Boko Haram
An ji cewa Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta yi magana kan batun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram, ISWAP ko wasu ƙungiyoyin masu aikata laifufffuka.
Manjo Janar Samaila Uba ya ce sojoji na ci gaba da matsin lamba kan ’yan ta’adda, tare da kashe wasu, kama waɗanda ake zargi da ceto mutanen da aka sace.
Rundunar ta ce ayyukanta ba su takaita ga Boko Haram da ISWAP ba, domin sun haɗa da masu garkuwa da mutane da sauran ’yan bindiga.
Asali: Legit.ng

