Kasurgumin Dan Bindiga da Yaransa 6 Sun Hadu da Abin da Ya Fi Karfinsu, Sun Mutu nan Take
- An kashe wani fitaccen jagoran ’yan bindiga, Kachalla Mu’azu, da wasu ’yan ƙungiyarsa shida a wani artabu tsakanin ƙungiyoyi a Zamfara
- An ce an kai musu harin kwanton bauna ne yayin da suke dawowa daga kasuwar Yankara a yankin Gusau
- An ruwaito cewa hukumomin tsaro na ci gaba da sa ido kan yankin bayan artabun, yayin da ake sa ran mutane za su samu sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - An kashe wani fitaccen shugaban dabar ’yan bindiga, Kachalla Mu’azu, da wasu manyan yaransa shida a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.
Rahotanni sun nuna cewa dan ta'addan, wanda ya addabi al'umma ya yi bankwana da duniya ne a wani artabu tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga masu hamayyada juma a Jihar Zamfara.

Source: Original
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba.
Yadda aka kashe dan ta'addan
A cewar Makama, lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7.30 na yammacin jiya Laraba, 7 ga Oktoba, a kusa da Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau ta jihar.
Ya ce Kachalla Mu’azu da mutanensa suna dawowa ne daga Kasuwar Yankara lokacin da mambobin wata dabar ’yan bindiga suka kai musu harin kwanton bauna a kan hanyar da suke bi.
Makama ya ce artabun da ya biyo baya ya yi sanadin mutuwar Mu’azu da wasu mutane shida daga cikin yaransa.
Kachalla Mu’azu ya shahara a Zamfara
Makama ya bayyana Mu’azu a matsayin wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga da ake zargi da hannu a ayyukan laifi da hare-haren da suka shafi al’ummomin Gusau da sauran sassan Jihar Zamfara, da kuma wasu yankunan Jihar Katsina.
“Ana sa ran mutuwar tasa za ta yi tasiri kan ayyukan ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke aiki a yankin Gusau, ko da yake har yanzu ba a fayyace ko kisan zai haifar da wani sauyi nan take a yanayin tsaro ba.

Kara karanta wannan
Ana cikin jimamin hatsarin jirgi, an shiga sansanin sojojin Najeriya an kashe sama da 10
“Mada wata matsuguni ce da ke gabashin ƙaramar hukumar Gusau, mai nisan kusan kilomita 32 daga garin Gusau, yayin da Yankara take kan hanyar Gusau zuwa Funtua.
“Ana sa ran hukumomin tsaro za su ci gaba da sanya ido kan yankin bayan artabun da aka ruwaito, tare da gano ƙarin bayanai kan ƙungiyoyin da suka yi artabun,” in ji Makama.

Source: Facebook
Rahoton kisan ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a Zamfara, inda ƙungiyoyin ’yan bindiga ke kai hare-hare, yin garkuwa da mutane a sassa daban-daban na jihar.
An kashe sojoji 12 a jihar Zamfara
Kun ji cewa akalla sojoji 12 da fararen hula biyar ne aka kashe da ’yan bindiga suka kai hari sansanin sojoji a ƙauyen Bindin a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Baya ga kashe rayuka 17 a harin, an ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane biyu zuwa maboyarsu da ba a san inda take ba.
Asali: Legit.ng
