Barazanar da ADC Ta Yi a Kaduna bayan Hana Ta Taro a Babban Filin Wasa

Barazanar da ADC Ta Yi a Kaduna bayan Hana Ta Taro a Babban Filin Wasa

  • Jam’iyyar ADC ta yi barazanar gudanar da gangamin siyasa a kan titunan Kaduna bayan gwamnatin jihar ta hana ta sakat
  • Jam’iyyar ta zargi gwamnatin jihar da nuna wariya, tana mai cewa APC ta yi amfani da filin yayin kamfen nata a watan Oktoba.
  • ADC ta ce hana ta filin wasan ba zai hana ta gudanar da ayyukanta ba, domin tana da ‘yancin gudanar da taron lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna – Jam’iyyar ADC ta yi barazanar gudanar da gangamin yakin neman zabe a kan titunan birnin Kaduna.

Hakan ya biyo bayan gwamnatin jihar na hana ta amfani da filin wasa na Ranchers Bees domin gudanar da shirye-shiryenta na ranakun 17 zuwa 18 ga watan Nuwamba.

ADC ta zargi APC da nuna wariya
Atiku Abubakar da mataimakinsa a zaben 2027, Rotimi Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Talata, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ana zargin za a yi gagarumar tarzoma a wajen kamfen din Tinubu a Kebbi

Zargin da ADC ke yi wa APC

Jam’iyyar adawar ta zargi gwamnatin jihar da amfani da kadarorin gwamnati wajen kawo cikas ga harkokin siyasa, inda ta tambayi dalilin da ya sa aka hana ta amfani da filin wasan.

ADC ta ce ta nemi izinin amfani da filin wasan daga gwamnatin jihar, amma Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta ki amincewa da bukatar a cikin wata wasika mai dauke da ranar 12 ga Nuwamba.

A cewar sanarwar, ma’aikatar ta bayyana cewa ana gudanar da aikin gyaran filin wasan ne a matsayin dalilin hana jam’iyyar amfani da shi.

ADC ta ce APC ta yi amfani da filin

Sai dai ADC ta nuna rashin gamsuwa da wannan bayani, tana mai cewa APC ta gudanar da bikin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a filin wasan a ranar 24 ga Oktoba, kasa da wata guda kafin lokacin da ita ma ta shirya amfani da wurin.

Kara karanta wannan

An rasa rai bayan rikici ya ɓarke tsakanin makiyaya da tawagar kamfen siyasa

Jam’iyyar ta bayyana hujjar gwamnatin a matsayin abin dariya, inda ta ce ta san dalilin da ya sa ake hana ta gudanar da taronta a wurin.

Ta yi zargin cewa APC na tsoron yawan jama’ar da ke halartar gangaminta a yankin Arewa, kuma ba ta son mazauna Kaduna su kwatanta karfin goyon bayan da take samu da na jam’iyyar adawar.

ADC ta zargi gwamnatin Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: Facebook

ADC ta yi barazanar komawa kan tituna

Duk da hana ta amfani da filin wasan, jam’iyyar ta ce ba za ta fasa shirye-shiryenta a Kaduna ba, tana mai cewa za ta gudanar da gangami a kan tituna idan gwamnatin jihar ba ta sauya matsayinta ba.

A cewar sanarwar, idan gwamnatin Kaduna ba ta ba ta damar gudanar da gangami cikin lumana a filin wasan ba, za ta yi amfani da ‘yancin da kundin tsarin mulki ya ba ta na yin taro cikin lumana a kan tituna.

ADC ta jaddada cewa gwamnati na iya hana ta amfani da wani wurin taro, amma ba za ta iya kwace wa ‘yan Najeriya ‘yancin gudanar da taron lumana ba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gobara ta kama a katafariyar ma'ajiyar babban dan kasuwa a jihar Kaduna

An zayyano matsalolin Atiku a 2027

Mun ba ku labarin cewa Segun Sowunmi ya ce ’yan Najeriya sun sha ƙin zaɓen Atiku Abubakar a zaɓukan shugaban ƙasa da ya tsaya takara.

Tsohon kakakin kamfen ɗin Atiku ya tambayi dalilin da ya sa matasan Arewa za su ci gaba da mara masa baya.

Sowunmi ya ce har yanzu ba a tabbatar da takarar Atiku a ƙarƙashin ADC ba, duk da ɗaukaka ƙarar da jam’iyyar ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.