Hanyar da Atiku Zai Samu Kuri'u cikin Sauki a Zaben 2027
- Phrank Shaibu ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar zai samu ƙarin ƙuri’u a zaɓen 2027 daga ’yan Najeriya
- Shaibu ya yi zargin cewa yunwa da talauci za su yi tasiri sosai wajen yanke shawarar masu zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa
- Ya kuma soki shirin gwamnatin Tinubu na ɗaukar masu tasiri a kafafen sada zumunta 4,000 domin yaɗa ayyukan da ta aiwatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Phrank Shaibu, mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan harkokin sadarwa, ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai kasance mafi sauƙi ga ubangidansa.
Shaibu ya yi hasashen cewa ’yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki za su kaɗa wa Atiku ƙuri’a, musamman waɗanda ba su gamsu da yanayin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Mic On Podcast, lokacin da aka tambaye shi yadda Atiku zai inganta kuri'un da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A zaɓen na 2023, Atiku ya samu kashi 29 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, duk da kasancewar Tinubu a kan mulki da kuma tsarin siyasar da yake da shi.
“Hanyar samun nasarar a bayyane take, kuma wannan zaɓen zai kasance ɗaya daga cikin mafi sauƙi ga Atiku Abubakar.” In ji shi.
Ya ce yunwa da talauci za su yi tasiri zaɓen 2027
Mai taimaka wa Atiku ya bayyana cewa yunwa da talauci za su taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar masu zaɓe a shekarar 2027.
Ya nuna kwarin gwiwar cewa ’yan Najeriya da ke neman sauƙin rayuwa za su mara wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa baya.
“’Yan Najeriya masu fama da yunwa da talauci, waɗanda ke fatan rayuwa za ta sake zama mai sauƙi, za su kaɗa wa Atiku ƙuri’u masu yawa a ranar 16 ga Janairu.” In ji shi.

Kara karanta wannan
Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu
Ya dage cewa ƙuri’un da Atiku ke sa ran samu za su fito ne daga mutanen da suka yi imanin cewa gwamnatin Tinubu ta gaza inganta yanayin rayuwarsu.
Shaibu ya kuma yi zargin cewa Tinubu da iyalansa, da kuma ministocinsa, sun san gazawar da yake zargin gwamnatin ta samu.
“Tinubu da kansa ya san cewa ya gaza. Matarsa ta san ya gaza. Ɗansa ya san ya gaza. Ministocinsa sun san ya gaza.” In ji shi.
Shaibu ya soki shirin ɗaukar masu tasiri 4,000
A yayin hirar, mai taimaka wa Atiku ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa gwamnati za ta ɗauki dubban masu tasiri a kafafen sada zumunta domin tallata nasarorinta.
Ya yi wannan tsokaci ne bayan kalaman Ministan Ayyuka, David Umahi, game da shirin ɗaukar masu tasiri 4,000 domin nuna ayyukan gwamnatin Tinubu ga jama’a.
Shaibu ya ce gwamnati da ta yi gagarumin tasiri a rayuwar ’yan ƙasa ya kamata ta iya nuna nasarorinta ba tare da dogaro sosai da masu tasiri a kafafen sada zumunta ba.

Source: Facebook
Atiku ya soki Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan
"Ku yafe mini," Tsohon gwamna ya fito ya nemi afuwar yan Najeriya kan kawo masu Tinubu a 2023
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya soki Tinubu ne kan matakin rangwamen farashin fetur na kwanaki 30, yana mai cewa shirin ba zai kawo sauki mai dorewa ga ’yan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng
