"Ku Yafe Mini," Tsohon Gwamna Ya Fito Ya Nami Afuwar Yan Najeriya kan Kawo Masu Tinubu a 2023

"Ku Yafe Mini," Tsohon Gwamna Ya Fito Ya Nami Afuwar Yan Najeriya kan Kawo Masu Tinubu a 2023

  • Tsohon gwamnan Edo, John Odigie Oyegun, ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan taimaka wa APC da Shugaba Bola Tinubu su hau mulki a zaɓen 2023
  • Oyegun ya ce zaɓen 2027 zai ba ’yan Najeriya damar gyara abin da ya kira kuskuren zaɓen 2023
  • Tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna ƙara jefa ’yan Najeriya cikin talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Edo, Cif John Odigie Oyegun, ya ba ’yan Najeriya haƙuri kan taimaka wa jam’iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu su hau mulki a babban zaɓen 2023.

Oyegun, wanda ya kasance shugaban jam’iyyar APC na ƙasa daga shekarar 2015 zuwa 2019 kafin ya sauya sheƙa zuwa ADC a shekarar 2026.

Oyegun.
Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban APC na kasa, John Oyegun Hoto: John Oyegun
Source: Twitter

A rahoton Daily Trust, Oyegun ya ce ’yan Najeriya na shan wahala sakamakon abin da ya kira “kuskure” na zaɓen Tinubu da APC a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Tunanin Tinubu ya mamaye zuciyar minista, yana zuwa har a cikin barci

Ya ce babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa ya ba ’yan Najeriya damar gyara wannan kuskure da kuma hanzarta ci gaban ƙasar.

Oyegun ya bayyana hakan ne a birnin Benin, lokacin da jam’iyyar ADC ta karɓi ɗan takararta na mataimakin shugaban ƙasa, Rotimi Amaechi, a wani taron tattaunawa da jama’a.

Oyegun ya nemi a ceto Najeriya

Oyegun ya ce:

“Yau, muna shan wahala a faɗin ƙasar nan sakamakon mummunan kuskuren da aka yi a shekarar 2023. Yanzu ne lokacin da za mu ceci ƙasar ta hanyar gabatar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku, da abokin takararsa, Rotimi Amaechi.
“Aikin ADC a yanzu shi ne ceton ƙasa. Eh, mun yi irin wannan kuskure, amma mun kawo Atiku, wanda yake da ƙwarewa sosai, da Amaechi, wanda ba ya tsoron kowa. An yaudare mu sau ɗaya, kuma ba za mu sake bari a yaudare mu ba,” in ji shi.

Sai dai Oyegun ya nuna damuwa kan yadda ake tsoratar da mutane a siyasar jihar Edo, musamman zargin barazanar amfani da bindigogin AK-47.

Kara karanta wannan

Atiku vs Tinubu: Jam'iyyar ADC ta shata layi, ta gindaya sharadi kan babban zaben 2027

Ya kuma tambayi ko irin wannan yanayin siyasa ne al’ummar jihar suke so, yana mai jaddada cewa ya kamata mutane su farka.

Amaechi ya soki manufofin Tinubu

A nasa jawabin, tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa suna ƙara jefa ’yan Najeriya cikin talauci a kullum.

Amaechi.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi a wurin taro Hoto: Chibuike Rotimi Amaechi
Source: Twitter

Amaechi ya jaddada cewa manufofin gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur, sun ƙara tsananta hauhawar farashi tare da ƙara nauyin matsin tattalin arziki a kan talakawa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Amaechi ya ragargaji magoya bayan APC

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi ya ce babu wanda zai sake zaben Bola Tinubu sai mahaukaci.

Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Ribas, ya zargi gwamnatin Tinubu da yin ayyuka saboda kudin da za su samu ba don amfanin jama’a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262