Zaben 2027: NDC Ta Hakura, Obi da Kwankwaso Za Su Samu Yadda Suke So
- Jam’iyyar NDC ta amince Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, su zaɓi wasu manyan jami’an kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa
- Shugaban jam’iyyar, Sanata Moses Cleopas, ya ce ana sa ran ƙaddamar da kwamitin a ranar 20 ga Nuwamba, idan babu wani cikas
- Cleopas ya kare jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Henry Seriake Dickson, daga zargin rashin goyon bayan tikitin Obi da Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar NDC ta warware rikicin da ya dabaibaye kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, bayan amincewa cewa ɗan takararta, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, za su zaɓi wasu manyan jami’an kwamitin.
Rikicin ya ɓarke ne tsakanin shugabancin jam’iyyar da wata ƙungiyar goyon baya da ke cikinta, mai suna OK Movement, kan yadda za a naɗa mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja.
A ƙarƙashin sabon tsarin, Obi da Kwankwaso za su zaɓi Darakta-Janar, Mataimakin Darakta-Janar na Arewa, Daraktan Kuɗi, Mataimakin Daraktan Kuɗi da Daraktan Yaɗa Labarai.
Ana sa ran ƙaddamar da kwamitin
Sanata Moses Cleopas ya ce shugabancin jam’iyyar ya yi nisa wajen tattaunawa da ɗan takararta na shugaban ƙasa da mataimakinsa domin tabbatar da cewa an gudanar da tsarin yadda ya kamata.
Cleopas ya ce idan babu wani cikas, za a bayyana sunayen mambobin kwamitin a ranar 20 ga Nuwamba.
Ya bayyana cewa jerin shawarwari da tattaunawar da aka gudanar tsakanin matakan shugabancin jam’iyyar ne suka jawo jinkirin sanar da kwamitin.
Cleopas ya kuma tabbatar da cewa Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar ya amince da wannan tsari.
A cewarsa, dole ne Obi da Kwankwaso su taka muhimmiyar rawa wajen kafa kwamitin, domin su ne za su jagoranci yaƙin neman zaɓe tare da tsayawa takara a ƙarƙashin tutar jam’iyyar.
Ya ce jinkirin da aka samu da gangan aka yi shi domin guje wa kura-kurai wajen kafa tsarin kamfen ɗin zaɓen da ya bayyana a matsayin mai muhimmanci ga makomar Najeriya.
Cleopas ya kare Dickson daga zargi
Shugaban jam’iyyar ya buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ke ƙoƙarin nuna cewa shugaban jam’iyyar, Sanata Henry Seriake Dickson, bai da cikakken goyon baya ga tikitin Obi da Kwankwaso.
Cleopas ya ce Dickson ya ƙi yin amfani da matsayinsa na jagoran jam’iyyar wajen zama ɗan takarar shugaban ƙasa, don haka yana goyon bayan nasarar jam’iyyar.
“Ƙirƙira da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa nauyi ne da ya rataya a wuyan shugabancin jam’iyya a matakin koli. Amma jam’iyyar ba za ta iya yin hakan ba tare da tuntubar ɗan takararta da mataimakinsa ba.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa, gara a ɗauki lokaci domin yin abu yadda ya kamata maimakon gaggawa da yin kuskure.

Source: Facebook
INEC ta cire sunan dan takarar NDC a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa INEC ta cire sunan ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, daga cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar guda 17 da ta fitar.
Matakin ya kara tabbatar da cewa akwai rikici a tafiyar Kwankwasiyya, wacce ke burin karbe mulkin jihar Kano daga gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya koma APC.
Asali: Legit.ng

