Kotu Ta Soke Zaben Dan Majlisar PDP Na 3 a Jihar Plateau

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majlisar PDP Na 3 a Jihar Plateau

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe mai zamanta a Jos ta soke nasarar zaɓen Dachung Musa Bagos, ɗan majalisar PDP mai wakiltar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas
  • Kotun a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, ta yi hukunci cewa Bagos ba jam'iyyar PDP ba ce ta tsayar da shi takara, inda daga ƙarshe ta ayyana ɗan takarar LP, Ajang Alfred, a matsayin wanda ya lashe zaɓen
  • Soke zaɓen Dachung ya zama karo na uku a jihar Plateau da kotun zaɓe ta soke zaɓen ƴan takarar jam'iyyar PDP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jos, jihar Plateau - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya mai zamanta a Jos, babban birnin jihar Plateau, ta soke zaɓen ɗan majalisar wakilai, Dachung Musa Bagos.

Bagos, wanda yake wakiltar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a majalisar wakilai an zaɓe shi ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Zaben 'Yar Majalisar PDP a Jihar Arewa, Ta Ba Dan Takarar APC Nasara

Kotu ta soke zaben dan majalisar PDP a Plateau
Kotu ta kwace kujerar Dachung Musa Bagos a jihar Plateau. Hoto: @dachungbagos
Asali: Twitter

Kotu ta soke zaɓen ɗan majalisa mai hawa biyu

Da take soke zaɓen Bagos a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP), Ajang Alfred, a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen, cewar rahoton The Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta yi hukunci cewa ɗan takarar na jam'iyyar PDP ba jam'iyyarsa ba ce ta zaɓe shi domin yin takara a zaɓen, rahoton The Nation ya tabbatar.

Bagos shi ne ɗan majalisa na uku na jam'iyyar PDP da aka soke zaɓensu a jihar a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Sauran biyun sun haɗa da Sanata Napoleon Bali mai wakiltar Plateau ta Kudu a majalisar dattawa da Peter Gyengdeng wanda yake wakiltar mazaɓar Barkin Ladi/Riyom a majalisar wakilai.

Dan Minista Ya Rasa Kujerarsa

Kara karanta wannan

Kotu Ta Rushe Nasarar Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar APC, Ta Ayyana Zaɓen a Matsayin Wanda Bai Kammalu Ba

A wani labarin kuma, Kotun sauraron ƙararrakin zaben 'yan majisun tarayya da na jiha ta jihar Neja ta tsige Joshua Gana daga kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya.

Joshua, ɗan tsohon ministan yaɗa labarai, Jerry Gana, shi ne ɗan takarar jam'iyyar PDP na mazaɓar Edati/Lavun/Mokwa ta tarayya a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel