‘Litar Mai Za Ta Iya Kai wa N2000’: An Fadi Illar da Atiku Zai Yi wa Talakawa
- Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin fetur na iya jawo litar mai ta kai Naira 2,000
- Oyedele ya ce cire tallafin fetur ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga asusun tarayya tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025
- Gwamnatin tarayya na shirin rage haraji da kuɗaɗen hanya, tare da ƙara tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi da rancen kasuwanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya yi gargaɗin matsalar da samu Najeriya idan aka dawo da tallafin mai.
Oyedele ya ce darajar canjin kuɗi na iya kaiwa Naira 3,000 kan dala guda cikin watanni kaɗan, yayin da litar fetur za ta iya kaiwa aƙalla Naira 2,000.

Source: Facebook
Oyedele ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani taron manema labarai kan tallafin fetur da aka gudanar a Abuja, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Bayan an mata rubdugu, jami'ar ABU ta canza shawara kan batun ƙarin kuɗin makaranta
Hasasehn da ministan kudi ya yi
Ministan ya ce hasashensu shi ne darajar canjin kuɗi na iya kusantar Naira 3,000 kan dala guda cikin watanni kaɗan.
Ya ce don haka farashin fetur da ake cewa ana tallafa wa zai kai aƙalla Naira 2,000 kan kowace lita. Wannan ya fi abin da ’yan Najeriya ke biya a yanzu.”
Ya ce:
“Tallafi ba ya rage kuɗin da ake kashewa wajen samar da fetur. Abin da yake yi kawai shi ne sauya yadda ake biyan kuɗin da kuma lokacin biyan sa. A baya ’yan Najeriya sun biya kuɗin wannan tallafi ta hanyar ƙarancin man fetur, hauhawar farashi da durƙushewar darajar kuɗi.”
Ministan ya ce dole ne a samar da kuɗin tallafi ta wata hanya domin jinkirta biyan albashi da fansho, ƙara haraji ko buga sababbin kuɗaɗe.
Ministan ya ce samar da sauƙi cikin gaggawa ta hanyar sadaukar da zaman lafiyar tattalin arziki na dogon lokaci zai zama hanya mafi tsada da gwamnati za ta kashe kuɗi.

Kara karanta wannan
Bayan fetur, Gwamnatin tarayya na shirin rage hauhawar farashin muhimman kayayyaki
Ya ce:
“Muna buɗe ƙofofinmu ga sabbin shawarwari. Amma duk wata shawara mai inganci dole ne ta amsa tambayoyi uku. Nawa za ta ci? Ta yaya za a samar da kuɗinta cikin ɗorewa? Kuma wane farashin fetur za ta samar? Za mu tattauna da gaskiya da duk wanda ya gabatar da shawara mai ƙididdiga bayyananniya.”

Source: Facebook
Amfanin da aka samu bayan cire tallafi
Oyedele ya ce cire tallafin fetur ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga asusun tarayya tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
Ya ce daga cikin wannan kuɗi, an raba Naira tiriliyan 10.4 ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.
Oyedele ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na nazarin matakan kawar da haraji da kuɗaɗen da ake karɓa ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke ƙara kuɗin sufuri da jigilar kayayyaki, domin rage wa jama’a raɗaɗin cire tallafin fetur.
Ya ce:
“Muna aiki tare da jihohi ƙarƙashin dokokin garambawul ga haraji na shekarar 2025 domin takaita haraji da kuɗaɗen da ake karɓa a kan tituna, waɗanda ke ƙara kuɗin sufuri da jigilar kayayyaki.

Kara karanta wannan
Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027
“Muna ƙara kuɗaɗen da ake warewa domin tallafin kuɗi ga gidajen da suka fi fuskantar talauci, da kuma samar da rance mai sauƙin ruwa ga ƙananan ’yan kasuwa da masu sayayya.”
A cewar ministan, gwamnatin tarayya na kuma rage kuɗaɗen ƙa’idojin gudanar da kasuwanci waɗanda ke ƙara kuɗin gudanar da harkokin kasuwanci, tare da haddasa hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka kai tsaye ko a fakaice.
'Mahaukata ne za su zabi Tinubu' - Amaechi
An ji cewa Rotimi Amaechi yana da ra’ayin cewa kuri’un Bola Tinubu suna wajen barayi da mahaukata a Najeriya .
Dan takaran mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar ADC ya ce mahaukaci ne zai zabi APC a takarar 2027.
Amaechi ya ce idan aka ga gwamnatin Tinubu tana aiki, kudin da za ta samu take hari ba cigaban jama’a ba.
Asali: Legit.ng