Fadar Shugaba Kasa Ta Fadi Mamakin da Tinubu zai Bayar a 2027
- Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Tinubu zai yi nasara a zaben shugaban ƙasa na 2027
- Bwala ya ce tazarar da Tinubu zai samu tsakaninsa da sauran ‘yan takara za ta kasance mai girma matuka, har mutane ba za su yarda da abin da suka gani ba
- Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin, inda ya mayar da martani kan tambayar abin da ya sa yake da yakinin Tinubu zai lashe zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaben shugaban ƙasa na 2027.
Bwala ya ce tazarar da shugaban ƙasar zai samu tsakaninsa da sauran ‘yan takara za ta kasance mai girma matuka.

Source: Twitter
Channels Television ta ruwaito cewa Bwala ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today, inda aka tambaye shi abin da ya ba shi kwarin gwiwar cewa Tinubu zai iya lashe zaben 2027.
Bwala ya kare Tinubu
Bwala ya ce tun kafin zaben 2023, alamu da kididdigar da ake gani ba su nuna cewa Tinubu ne zai samu nasara ba.
Ya ce jam’iyyar da ke mulki a lokacin ba ta yi wa Tinubu aiki yadda ya kamata, yayin da wasu manufofin da aka gabatar gabanin zaben suka kasance masu illa ga damar samun nasararsa.
Ya ƙara da cewa akwai gwamnoni da ake zargin ba su ji daɗin wasu abubuwa da suka faru a lokacin ba.
Bwala ya ce ko a lokacin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC ma, Tinubu ya fuskanci ƙalubale, inda ya ce da an iya hana shi samun tikitin takarar shugaban ƙasa.
Nasarar Tinubu za ta ba da mamaki
Da yake magana kan abin da yake sa ran faruwa a zaben 2027, Bwala ya ce Tinubu zai yi tazarar da ba za a yi tsammani ba tsakaninsa da sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa.
Vanguard ta wallafa cewa ya ce:
“Bari in gaya muku kuma in faɗa a sarari, zan yi farin cikin dawowa domin ganin hakan, tazarar da Shugaba Bola Tinubu zai yi da kowane ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan takara za ta kasance mai girma har ba za ku yarda da ita ba.”

Source: Twitter
Bwala ya ƙara tambayar yawan gwamnoni da suka koma bayan Tinubu, yana mai cewa goyon bayan da suke bayarwa na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsarin siyasar shugaban ƙasar a jihohinsu.
An zargi APC da takura 'yan adawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa jigo a jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya zargi gwamnatin tarayya karkashin APC da samar da cikas ga ‘yan adawa gabanin babban zaben 2027.
Buba Galadima ya yi zargin cewa ana hana ‘yan takarar jam'iyyun adawa yin yakin neman zaɓe cikin ‘yanci a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya ce wasu ‘yan adawa na fuskantar hare-hare a duk lokacin da suka je wasu yankuna, yana mai cewa gwamnatin APC na son mayar da rayuwa mai wahala ga wadanda suke adawa da ita.
Asali: Legit.ng


