2027: APC Ta na Goyon Bayan Hana Pantami, Tsohon IGP da Sauransu Takara
- Jam’iyyar APC ta rubuta wa INEC wasiƙa, tana neman aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan amfani da rajistar mambobin jam’iyyun siyasa
- APC ta ce jam’iyyun da suka gaza miƙa rajistar mambobinsu ta zamani cikin wa’adin doka, ya kamata a hana su tsayar da ‘yan takara
- Jam’iyyar ta buƙaci INEC ta tabbatar da cewa masu rajista ne kawai za su kaɗa ƙuri’a ko neman takara a zaɓen cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta rubuta wa Hukumar zabe ta Ƙasa (INEC), tana neman ta gaggauta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.
APC na magana ne kan miƙa rajistar mambobin jam’iyyun siyasa da kuma amfani da ita a zaɓen fidda gwani, tarukan jam’iyyu da manyan tarukansu.

Source: Twitter
Hakan na cikin wasiƙar mai ɗauke da ranar 9 ga Oktoba, 2026, wadda shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Surajudeen Ajibola Basiru, da jam'iyyar ta wallafa a X.

Kara karanta wannan
INEC ta raba gardama, ta fadi matakin dauka kan jam'iyyun da suka karya dokar zabe
Bukatar APC ga hukumar INEC
APC ta buƙaci hukumar ta aiwatar da hukuncin bisa tanade-tanaden doka domin tabbatar da adalci a zaben 2027.
Jam’iyyar ta kuma nemi a yi amfani da matakan da doka ta tanada kan rashin bin ƙa’ida, ciki har da hana duk jam’iyyar da ta saɓa ƙa’idar tsayar da ‘yan takara a babban zaɓe.
APC ta buƙaci INEC ta ɗauki matakai uku, na farko, ta aiwatar da hukuncin bisa abin da ya ƙunsa da kuma tasirinsa na shari’a.
Na biyu, ta tantance ko kowace jam’iyyar siyasa ta miƙa rajistar mambobinta ta zamani cikin wa’adin da doka ta kayyade, sannan ta yi amfani da hukuncin da sashe na 77(7) ya tanada ga waɗanda suka gaza.
Na uku, ta tabbatar da cewa mambobin da sunayensu ke cikin rajistar da aka miƙa wa hukumar ne kawai za su kaɗa ƙuri’a ko kuma su tsaya takara a zaɓukan cikin gida na jam’iyyunsu.

Kara karanta wannan
Atiku vs Tinubu: Jam'iyyar ADC ta shata layi, ta gindaya sharadi kan babban zaben 2027
Jam’iyyar ta yi nuni da sashe na 77(4), wanda ya ce: “Kowace jam’iyyar siyasa za ta miƙa wa hukumar wannan rajista, ba ƙasa da kwanaki 21 kafin ranar da aka sanya domin zaɓen fidda gwani, tarukan jam’iyya ko manyan tarukanta ba.”
APC ta ƙara da cewa sashe na 77(5) ya bayyana cewa:
“Mambobin da sunayensu ke cikin rajistar ne kawai za su cancanci kaɗa ƙuri’a ko tsayawa takara a zaɓen fidda gwani, tarukan jam’iyyu da manyan tarukansu.”
An yanke hukuncin ne a ranar 24 ga Satumba, 2026, a shari’ar INEC da Zenith Labour Party (Lambar Shari’a SC/CV/495/2026).
Kotun ta tabbatar da sashe na 77 na Dokar Zaɓe ta 2026, tare da soke umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya ayyana sashe na 77(5) zuwa (7) da na 84(2) na dokar, da kuma sashe na biyu na jadawalin ayyukan INEC da aka yi wa gyara domin babban zaɓen 2027, a matsayin waɗanda suka saɓa wa kundin tsarin mulki.
INEC za ta fadi makomar Pantami da sauransu
Mun ba ku labarin cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta bayyana matsayarta kan makomar wasu ‘yan takara da hukuncin Kotun Koli kan tsarin zaben fitar da gwani ya shafa.
Daga cikin ‘yan siyasar da ake ta ce-ce-ku-ce kan makomarsu akwai Farfesa Isa Ali Pantami a Gombe, Muhammad Nami a Neja, Mohammed Adamu a Nasarawa.
Asali: Legit.ng