2023: Jerin Jihohi 28 da Za a Yi Zaben Gwamnoni a Najeriya a Ranar Asabar

2023: Jerin Jihohi 28 da Za a Yi Zaben Gwamnoni a Najeriya a Ranar Asabar

 • Yayin da zaben gwamnoni ya gabato, yana da muhimmanci a san adadin jihohin da za a yi zabe a Najeriya
 • Akalla akwai jihohi 28 da za a kada kuri’u a gobe Asabar 18 ga watan Maris a Najeriya bayan dage zaben daga 11 ga watan na Maris
 • Rahoto ya bayyana wadannan jihohin da kuma wasu jihohin da ba za a yi zaben gwamna ba a ranar ta Asabar

Najeriya - Bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, sakamako daga hukumar zabe ta INEC ya fito, wadanda basu ci zabe ba sun bayyana tafiya kotu.

Baya ga haka, sauran zaben jihohi; inda za a zabi sabbin gwamnoni ko kuma masu komawa da kuma ‘yan majalisun dokoki na jiha.

‘Yan Najeriya za su fito ne domin kada kuri’unsu a ranar Asabar 18 ga watan Maris, bayan dage zaben daga ranar 11 ga watan na Maris, Channels Tv ta tattaro.

Jihohin da za a kada kuri'u a Najeriya
Hoton mata na kada kuri'arta a rumfar zabe | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Gaba daya, jam’iyyun siyasa 18 ne ke da ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisu a Najeriya, ba a dukkan jihohin kasar bane kuma za a yi zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa wasu jihohin ba za a yi zabe ba

A bayyane yake, akwai jihohi 28 da za a kada kuri’u a Najeriya cikin 36 saboda akwai jihohin da zabensu ya bambanta da saura.

Kamar jihohin Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Osun da Ondo, duk suna da lokutan yin zabensu na daban ba na ranar Asabar mai zuwa ba.

Samun mabambantan lokacin zabe a jihohin yana da nasaba da hukunce-hukuncen kotu da suka sanya ake yin zaben daban.

Sai dai, zaben ‘yan majalisun jihohi a tare ake yi, kuma za a zabi ‘yan majalisu 993 a fadin jihohin Najeriya, kamar yadda bayanan INEC suka nuna.

Jihohin da za a yi zaben gwamnoni a Najeriya

 1. Abia
 2. Adamawa
 3. Akwa Ibom
 4. Bauchi
 5. Benue
 6. Borno
 7. Kuros Riba
 8. Delta
 9. Ebonyi
 10. Enugu
 11. Gombe
 12. Jigawa
 13. Kaduna
 14. Kano
 15. Katsina
 16. Kebbi
 17. Kwara
 18. Legos
 19. Nasarawa
 20. Neja
 21. Ogun
 22. Oyo
 23. Filato
 24. Ribas
 25. Sokoto
 26. Taraba
 27. Yobe
 28. Zamfara

An tura EFCC jihohin Kano, Jigawa da Katsina

A jajiberin zabe, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayyana tura jami’anta bangarori daban-daban na jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

Wannan na zuwa ne a shirin hukumar na tabbatar da an yi zabe cikin tsanaki a jihohin da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.

An samu hargitsi a zaben shugaban kasa da aka yi a wasu jihohin Najeriya, ciki har da jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel