Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi kan Sababbin Hanyoyin da 'Yan Ta'adda Suka Bullo da Su
- Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce ƙungiyoyin ’yan ta’adda a Afirka na ƙara amfani da sababbin fasahohi wajen gudanar da ayyukansu
- Ta yi kira ga ƙasashen Afirka su ƙarfafa musayar bayanan sirri, tsarin gano barazana tun da wuri da samar da isasshen kuɗin tsaro
- Ministar ta jaddada muhimmancin gyara da mayar da mutanen da ta’addanci ya shafa cikin al’umma, da kuma magance rashin aikin yi tsakanin matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ƙungiyoyin ’yan ta’adda a Afirka ke ƙara amfani da sabbin fasahohi wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamnatin ta yi kira ga ƙasashen nahiyar su ƙarfafa musayar bayanan sirri da samar da kuɗaɗen yaƙi da matsalar tsaro.

Source: Twitter
Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.
An fitar da sanarwar ne bayan jawabin da ta gabatar a wajen buɗe taron tuntuba kan inganta ayyukan tsarin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka a Abuja.
’Yan ta’adda na amfani da sababbin fasahohi
Odumegwu-Ojukwu ta ce ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙara amfani da sababbin fasahohi wajen gudanar da ayyukansu, yayin da suke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan ta’addanci ta hanyar manyan laifuffukan da suka shafi ƙasashe daban-daban da kuma zirga-zirgar kuɗaɗen haram.
Ta nuna damuwa kan ƙaruwar ta’addanci a nahiyar Afirka, tana mai cewa wannan yanayi na buƙatar ƙasashen nahiyar su ɗauki ƙarin nauyin magance matsalolin tsaro.
Ministar ta ce ya zama dole a ƙarfafa tsarin tsaro da ake da shi domin ya dace da sababbin barazanar da ke tasowa.
Ta nemi ƙasashen Afirka su ƙara tallafin tsaro
Yayin da barazanar tsaro a yankuna daban-daban ke ƙaruwa, Odumegwu-Ojukwu ta yi kira da a samar da tsarin zaman lafiya da tsaro na Afirka mai ƙarfi, isasshen kuɗi da kuma dogaro da kai.
Ta ce ya kamata ƙasashen nahiyar su ƙarfafa musayar bayanan sirri, inganta hanyoyin gano barazana tun da wuri da kuma tallafa wa ƙoƙarin sasanta rikice-rikice da ’yan Afirka ke jagoranta.
Ta kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa Tsarin Gargaɗin Farko na Nahiyar Afirka, ayyukan sasanta rikice-rikice na Tarayyar Afirka da kuma Tsarin Bita tsakanin Ƙasashen Afirka (APRM).
Magance matsalolin al’umma na da muhimmanci
Ministar ta ce ya kamata a mayar da hankali kan korafe-korafen al’umma, rashin aikin yi tsakanin matasa da kuma ƙarfafa ƙarfin al’umma wajen fuskantar barazanar tsaro.
Ta bayyana cewa samar da ingantattun tsare-tsaren zaman lafiya a matakin ƙasa da ƙarfafa musayar bayanan sirri tsakanin ƙasashen Afirka zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro.

Source: Twitter
Sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun dakile wani hari da mayakan kungiyar ’yan ta’addar Lakurawa suka kai a jihar Kebbi.
Dakarun sun samu nasarar dakile harin ne da 'yan ta'addan suka kai a sansanin sojoji na FOB Maiyama, a jihar Kebbi.
Asali: Legit.ng

