Yan Adawan Najeriya Sun Yi Rashi, Wani Babban Jigo a PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An tabbatar da rasuwar daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP, Cif Daniel Osi Orbih a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2026
- Rahotanni sun nuna cewa Orbih, yana da alaka ta kut-da-kut da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, Nyesom Wike
- Iyalan marigayin sun roki ’yan uwa, abokai da masoya da su ci gaba da tunawa da su a cikin addu’o’insu yayin da suke cikin jimamin wannan babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Rahotannin da muka ssnu yanzu haka sun nuna cews wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Cif Daniel Osi Orbih, ya riga mu gidan gaskiya.
Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwar cikin kaduwa da mika wuya ga kaddarar Allah, a wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar jigon PDP a Edo
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lauya, Barista Francis Udukhomoi Orbih, Esq., ne ya gsyinsanya hannu kan sanarwar a madadin iyalan Orbih.
An ruwaito cewa Orbih, wanda ke da alaka ta kut-da-kut da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, Nyesom Wike, ya rasu ne a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026.
A cewar sanarwar, marigayin ya mutu ya bar matarsa, Mrs Florence Orbih; ’ya’yansa, Ms Winifred Anwosiobor Orbih da Dr Mildred Omonemi Orbih; da ’yan’uwansa maza da mata, da kuma sauran ’yan uwa na dangi.
Iyalansa sun roki a masu addu'a
Iyalan sun roki ’yan uwa, abokai da masoya da su ci gaba da tunawa da su a cikin addu’o’insu yayin da suke kokarin shawo kan radadin rashin da suka yi.
“A wannan lokaci mai matukar wahala, muna rokon ’yan uwa, abokai da masoya da su tuna da daukacin iyalan mu a cikin addu’o’insu yayin da muke jimamin wannan babban rashi,” in ji sanarwar.
Iyalan sun kara da cewa za a sanar da karin bayanai, ciki har da shirye-shiryen jana’izar marigayin a lokacin da ya dace, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Marigayin na da kusanci da Ministan Abuja
Marigayi Cif Daniel Orbih, wanda aka fi sani da jajircewa da kuma kwazo wajen gudanar da harkokin siyasa a shiyyar Kudu maso Kudu na Najeriya, ya kasance amintaccen aboki kuma jigo na kusa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen gina jam'iyyar PDP a Jihar Edo da kuma fadin kasar baki daya ta hanyar dabarunsa na siyasa da jajircewa.

Source: Twitter
Tsohon sanata daga Borno ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Borno ta Tsakiya a Majalisar dattawan Najeriya, Kaka Mallam Yale, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya.
Dansa mai suna Ibrahim Yale ya bayyana cewa mahaifin na su ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno bayan fama da jinya.
Rasuwar tasa ta jawo jimami a Jihar Borno, musamman tsakanin al’ummar Borno ta Tsakiya da waɗanda suka yi aiki tare da shi a lokacin da yake majalisar dokoki.
Asali: Legit.ng

