Yakin Biyafara: Gwamnati Ta Tuno Zancen Kisan Gillar da Aka Yi Shekaru 59 da Suka Wuce
- Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta fito ta amsa cewa shakka babu an yi wa mutanen Asaba kisan gilla
- A lokacin da ake yakin basasa, sojoji sun kashe dinbin mutanen da babu ruwansu a yankin na Neja Delta
- Gwamnan Delta ya ce Najeriya za ta amsa laifin abin da aka ayi a shekarae 1967 domin a kama hanyar sasanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Delta - Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin ayyana kokarin sasanci game da wani kisan gillar da aka yi lokacin yaki.
Mai girma gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya tabbatar da wannan a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba 2026.

Source: Facebook
An yi bikin tunawa da kisan kiyashi a Asaba
Punch ta ce Rt. Hon. Oborevwori ya yi jawabi a wajen bikin cika shekaru 59 da kisan gillar da aka yi wa mutanen Asaba.
Sakataren gwamnatin Delta, Dr Kingsley Emu ya wakilci Mai girma gwamnan a wajen taron da aka yi a shekarar bana.
A lokacin da ake cikin yakin basasa da aka fi sani da biyafara, an yi wa daruruwan mutane kisan gilla a garin Asaba.
Hikimar yarda an yi kisan gillar
Gwamna Oborevwori ya ce yarda da gwamnati ta yi cewa an yi wannan danyen aiki zai taimaka wajen huce takaici.
Oborevwori yana ganin wannan ne matakin farko da za a bi a sasanta, ya ce gwamnatin jiha tuni ta yarda an yi kisan gillar.
"Yarda a hukumance daga Gwamnatin Najeriya cewa lamarin ya auku yana da muhimmanci.
"Dama can jihar Delta ta yarda wannan masifa ta faru. Najeriya za ta amince da hakan, mun yi imanin cewa duniya ma za ta yarda."
- Gwamna Sheriff Oborevwori
Gwamnan Delta ya kara da cewa Gwamnatin Najeriya za ta ayyana shirin sasanci, kuma yana mai fatan hakan za ta faru.
Daily Post ta rahoto shi yana cewa gwamnatin jiha za ta cigaba da goyon bayan duk wani yunkuri na yarda an yi kisan gillar.
Ya ce har abada bai kamata kabilanci ko akidar siyasa ko wani zargi ya zama silar kashe mutune haka kurum a Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Mutanen gari sun fadi abin da ya faru lokacin da jirgin sojojin Najeriya ya yi hatsari
Shawarar gwamnan Delta da kukan Obasanjo
Gwamnan Delta ya kuma bada shawarar a guji yin gadon kiyayya, sai dai duk da haka ya ce akwai bukatar a dauki darasi.
Hakan yana zuwa ne bayan an ji tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana kokawa da abin da ya faru a Asaba.
Janar Obasanjo mai ritaya ya ce kisan gillar da aka yi yana cikin abubuwan ban takaici da suka faru da ake yakin basasa.

Source: Getty Images
Haduran jirgin sojoji a Najeriya
Daga shekarar 2021 zuwa Oktoba 2026, kun samu rahoto cewa Najeriya ta samu akalla haɗurran jiragen sojin sama akalla 10.
Haduran sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 68 tare da rasa dukiya mai dinbin yawa da kayan yaki da Najeriya take ji da su.
A irin haka aka rasa Hafsun sojoji, Janar Ibrahim Attahiru da manyan jami’ai a 2021 kafin hadarin da aka yi kwanan a Ondo.
Asali: Legit.ng
