'Ni na Yi Aiki Amma Su Ake Yabawa': Amaechi Ya Yi wa Tinubu, Sanwo-olu gori
- Rotimi Amaechi ya ce shi ne ya gina tashar ruwa mai zurfi ta Lekki daga farko har kammala, yana zargin Tinubu da Sanwo-Olu da karɓar yabo
- Tsohon ministan sufuri ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta amince da gina tashoshin ruwa masu zurfi, ciki har da tashar Lekki
- Amaechi ya ce gwamnatin ADC za ta farfado da ayyukan tashoshin ruwa na Bonny, Akwa Ibom da Warri, tare da bai wa Gelegele fifiko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, Rotimi Amaechi, ya ce shi ne ya gina tashar ruwa mai zurfi ta Lekki.
Amaechi ya yi ikirarin cewa ya gina tashar daga farko har ƙarshe, yana zargin Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu, da karɓar yabo.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron masu ruwa da tsaki na ADC a Edo, yayin da yake amsa tambaya kan tashar Gelegele, cewar Vanguard.
An tambaye shi ko gwamnatin ADC za ta bunƙasa tashar Gelegele zuwa matsayin tashar ruwa mai zurfi ta Lekki idan ta lashe zaɓe.
Tsohon ministan sufuri ya ce gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ce ta amince da gina tashoshin ruwa masu zurfi da dama.
Ya ce tashar Lekki na cikin ayyukan, duk da cewa ra’ayin gina tashar ya samo asali ne tun kafin gwamnatin Buhari.
Amaechi ya ce ya jagoranci aikin gina tashar ne a lokacin da yake ministan sufuri, har aka kammala aikin gaba ɗaya.
Ya ce ya yi murabus ne domin neman takarar shugaban ƙasa, sannan Sanwo-Olu ya samu Buhari ya zo ya ƙaddamar da tashar.
Amaechi ya zargi Sanwo-Olu, Tinubu da wasu da ikirarin cewa su ne suka gina tashar, duk da cewa a cewarsa, ba su ziyarci wurin ba lokacin ginin.

Kara karanta wannan
Amaechi ya fayyace saukin da za a samu tun shekarar farko idan Atiku ya kafa gwamnati
Ya ce:
"Na gina tashar ruwa mai zurfi ta Lekki daga farko har ƙarshe. Na kammala ta gaba ɗaya, amma na yi murabus domin neman shugaban ƙasa.
"Lokacin ƙaddamar da ita, Sanwo-Olu da wasu, ciki har da Tinubu, suna cewa su ne suka gina ta. Babu ɗayansu da ya ziyarce ta tun farko."
Ya bayyana cewa Buhari ne ya amince da gina tashar, amma ra’ayin aikin ya samo asali ne daga gwamnatin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.
"Buhari ya amince da gina tashar, amma ainihin ra’ayin aikin na Obasanjo ne, duk da cewa gwamnatin Buhari ce ta gina ta,” Amaechi ya ce.
Tsohon gwamnan Rivers ya ce gwamnatin Buhari ta kuma amince da tashoshin ruwa masu zurfi a Bonny, Akwa Ibom da Warri.
Sai dai ya ce matsalar samun kuɗi ta hana wasu daga cikin ayyukan fara aiki yadda aka tsara.
Amaechi ya ce an tsara tashar Bonny mai zurfin mita 18, yayin da wurin da aka tsara tashar Akwa Ibom ke da zurfin ruwa tsakanin mita 17 zuwa 18.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027
Mulkin Tinubu: An caccaki kalaman Amaechi
An ji cewa hadimin shugaban kasa ya soki Rotimi Amaechi kan cewa manufofin tattalin arzikin Bola Tinubu sun haddasa rasuwar mahaifiyarsa.
Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan sadarwa da manufofi ya zargi Amaechi da yada labaran karya da kalaman siyasa masu neman jawo hankalin jama’a.
Ya ce har mutumin da ke ba Peter Obi shawara ba zai yarda cewa manufofin Tinubu ne suka kashe mahaifiyar Amaechi ba.
Asali: Legit.ng
