Atiku Ya Gano Babban Shirin Tinubu bayan Sanar da Rage Farashin Mai
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki rangwamen man fetur na kwanaki 30 da Gwamnatin Tarayya ta shirya
- Atiku ya ce rangwamen wani shiri ne na siyasa kafin zaɓe, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da shi wajen yaudarar ’yan Najeriya ba
- Ya ce Gwamnati ta kamata ta samar da tallafi mai ɗorewa, tare da rage farashin man fetur da inganta rayuwar ’yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da shirin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur na kwanaki 30 a gidajen mai na NNPC.
Atiku ya bayyana shirin a matsayin matakin wucin gadi da gwamnati ta ɗauka saboda matsin lamba, wanda ba zai iya gyara matsalar tsadar man fetur ba.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Dabarun Yaƙin neman zaɓen ADC, ya fitar, Atiku ya soki matakin gwamnatin Tinubu, cewar Punch.
Shirin Tinubu da Atiku ya gano
Ya ce ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na amfani da rangwamen man fetur a matsayin abin jan hankalin ’yan Najeriya abu ne na sakaci da kunya.
Atiku ya ce gwamnati ta kalli ’yan Najeriya suna fuskantar matsanancin wahala tsawon lokaci ba tare da samar musu da tallafi mai ma’ana ba.
Ya ce yayin da zaɓe ke ƙara kusantowa, Shugaba Tinubu ya fara gabatar da rangwamen wucin gadi a cibiyar matsalar tsadar rayuwa.
Atiku ya ce ya yi watsi da rangwamen da aka tsara na wata guda, yana mai cewa ’yan Najeriya ba wawaye ba ne da za a ba su rangwamen man fetur na wata guda.
Ya ce bayan shekaru ana fuskantar tsadar man fetur, gwamnati na tsammanin ’yan Najeriya za su manta da wahalar da suka sha da zarar rangwamen ya ƙare.
Atiku ya bayyana shirin a matsayin abin kunya da rashin tausayi, yana mai cewa ba wani cikakken tsarin tattalin arziki ba ne.
Ya ce rangwamen na kwanaki 30 tamkar bandeji ne na siyasa da aka ɗora kan raunin da gwamnatin ta taimaka wajen haifarwa.

Source: Getty Images
Fargabar da Atiku ke yi a Najeriya
Ya ce farashin abinci zai ci gaba da hauhawa, yayin da gwamnati ba za ta iya samar da sauƙi na wata guda sannan ta yi tsammanin yabo ba.
Atiku ya lura cewa rangwamen zai kasance ne kawai a gidajen man NNPC, yayin da gwamnati ba ta bayyana adadin da za a rage kowace lita ba.
Ya kuma ce gwamnati ba ta tabbatar da cewa rangwamen da masu motocin haya za su samu zai sa su rage kuɗin sufuri ga fasinjoji ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce sauya matsayar gwamnati kwatsam kan wannan batu na jin daɗin jama’a ya nuna cewa ta amince da matsalar da ’yan Najeriya suka sha.
Ya ce matakin ya kuma fallasa raunin ikirarin gwamnati na cewa ba zai yiwu a samar da tallafi mai ma’ana ba.

Kara karanta wannan
"Yan Najeriya ba su cancanci haka ba," Atiku ya sake aika sako mai ɗaga hankali ga Tinubu
Fadar shugaban kasa ta caccaki Amaechi
Mun ba ku labarin cewa hadimin shugaban kasa ya soki Rotimi Amaechi kan cewa manufofin tattalin arzikin Bola Tinubu sun haddasa rasuwar mahaifiyarsa.
Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan sadarwa da manufofi ya zargi Amaechi da yada labaran karya da kalaman siyasa masu neman jawo hankalin jama’a.
Ya ce har mutumin da ke ba Peter Obi shawara ba zai yarda cewa manufofin Tinubu ne suka kashe mahaifiyar Amaechi ba.
Asali: Legit.ng

