"Yan Najeriya ba Su Cancanci Haka ba," Atiku Ya Sake Aika Sako Mai Ɗaga Hankali ga Tinubu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza kare ’yan Najeriya daga tsananin matsin tattalin arziki
- Atiku ya soki manufofin gwamnati kan man fetur da sauran kayayyakin masarufi, yana mai cewa sun kara tsadar rayuwa
- Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce shirin jam’iyyarsa zai rage farashin man fetur da kuma nauyin tsadar rayuwa ga ’yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaza wajen sauke daya daga cikin muhimman nauyin gwamnati.
Atiku ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta gaza kare talakawan Najeriya daga matsanancin yanayin tattalin arziki.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
'Kiran 'Bola' da Atiku ke yi wa Tinubu na neman saka shakku kan ingancin zabensa'
Atiku ya ce jawabin Shugaba Tinubu na Ranar ’Yancin Najeriya ya nuna yadda gwamnatinsa ta nisanta kanta daga hakikanin rayuwar al’umma ta yau da kullum.
Atiku ya soki manufofin Tinubu
Atiku ya ce shugaban kasar ya yi magana kan wadata yayin da yake kare wasu manufofin da suka sa fetur da sauran muhimman kayayyaki ke kara tsada.
Ya kuma soki yadda Tinubu ya bayyana tallafin man fetur a matsayin wani abu da ake “kamuwa da shi” kamar jaraba.
Atiku ya kuma kalubalanci ikirarin shugaban kasar cewa ana biyan albashi da fansho “a kan lokaci kuma cikakke”, yana mai cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya na korafin jinkirin albashi, yayin da ’yan fansho ke ci gaba da gudanar da zanga-zanga.
Atiku ya kawo misalin Jamus
Atiku ya ce Jamus ta rage harajin man fetur da dizal da Yuro €0.17 kan kowace lita daga Oktoba zuwa Disamba, matakin da ya kiyasta zai lakume Yuro biliyan 2.5, yayin da farashin fetue a gidajen mai ya fara raguwa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027
“Idan man fetur ya kara tsada, sufuri ma zai kara tsada. Idan kudin sufuri ya tashi, farashin abinci da sauran muhimman kayayyaki zai karu. Wahalar za ta bi ’yan Najeriya daga gidan mai zuwa kasuwa har zuwa cikin gidajensu.
“Jamus ta fahimci cewa idan farashin man fetur ya jefa iyalai cikin matsin lamba, dole gwamnati ta dauki mataki. ’Yan Najeriya ma sun cancanci irin wannan tausayi da gaggawar daukar mataki.
“Shirinmu shi ne dawo da tallafin da aka tsara kuma aka tanada a kasafin kudi, tare da tsauraran matakan bincike da kuma tabbatar da cewa tallafin ya rage farashin man a gidajen mai.
- Atiku Abubakar.

Source: Twitter
Atiku ya yi alkawarin rage tsadar rayuwa
Atiku ya kuma sake nanata alkawarin cewa gwamnatinsa za ta rage tsadar rayuwa, yana mai cewa yan Najeriya ba su cancanci wahalhalun da suke fuskanta a mulkin Tinubu na.
“Tinubu ya sanya rayuwa ta zama mai tsada fiye da kima sannan ya kira wahalar da kuke ciki da yunkurin gyara. Zan sake sanya rayuwa ta zama mai sauki," in ji shi.
Atiku zai magance magudin zabe
Kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi alkawarin kawo karshen magudin zabe da karfafa ‘yancin INEC idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.
Wazirin Adamawa ya bayyana wasu muhimman sauye-sauyen zabe da zai aiwatar domin dawo da kwarin gwiwar masu kada kuri’a ga tsarin dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng