Gwamnan Arewa Ya Je wurin Tinubu, Ya Fada Masa Abin da Mutanen Jiharsa Za Su Yi a Zaben 2027
- Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya ce gba daya jihar za ta mara wa APC baya a zaɓen 2027, tare da zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Kefas ya ce ayyukan gwamnatin tarayya a tsaro, ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa sun ƙara wa Tinubu farin jini a jihar
- Gwamnan ya ce al’ummar Taraba sun tabbatar masa da cewa za su zaɓi Tinubu da gaba daya kuri'unsu a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba, Nigeria - Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi ikirarin cewa gaba daya jiharsa “100%” ta jam’iyyar APC ce, yana mai cewa mazauna jihar za su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Gwamna Kefas ya ce ayyukan gwamnatin tarayya a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa sun ƙara ƙarfafa goyon bayan Shugaban Ƙasa, yana mai cewa mazauna Taraba sun fara ganin tasirinsu.

Source: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Abin da ya kai gwamnan wurin Tinubu
Kefas, wanda ya bayyana kansa a matsayin jagoran APC a Taraba, ya ce ya je Fadar Shugaban Ƙasa ne domin tarbar Tinubu da kuma jajanta masa kan hatsarin jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya da ya faru a jihar Ondo.
Ya bayyana hatsarin, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an soji da sauran ’yan Najeriya, a matsayin babban bala’i na ƙasa da ya kamata a nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa, Rundunar Soji da iyalan waɗanda suka rasu.
“Ni ma jagoran APC ne a jihata, don haka na zo ne domin yiwa Shugaban Ƙasa barka da dawowa gida da kuma jajanta masa kan lamarin hatsarin jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya, da jami’ai da sojoji da ’yan ƙasar nan da abin ya shafa,” in ji Kefas.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Kefas ya magantu kan Tinubu
Da yake magana kan siyasa da yadda gwamnatin Tinubu ke gudanar da mulki, gwamnan ya ce ayyukan da Shugaban Ƙasar ke yi sun ci gaba da yin tasiri a rayuwar mazauna Taraba.
A cewarsa, alfanun da ake samu ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatinsa sun ƙara wa al’umma kwarin gwiwa kan jagorancin Shugaban Ƙasa.
“Dukkan ayyukan tallafi da goyon bayan da Shugaban Ƙasa yake bayarwa, jama’a suna ganin tasirinsa, tun daga tsaro zuwa ilimi kyauta, tsarin kiwon lafiya da ababen more rayuwa,” in ji shi.
Duka mutanen Taraba suna tare da APC
Kefas ya ce goyon bayan da Shugaban Ƙasa ke bai wa Taraba ya sa mazauna jihar suka gamsu cewa gwamnatin tarayya tana amsa bukatunsu ta hannun gwamnatin jihar.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa al’ummar jihar sun tabbatar masa da goyon bayansu ga Tinubu yayin da ƙasar za ta koma rumfunan zaɓe a 2027.
“Don haka mutane ba su da wata shakka, kuma sun tabbatar da cewa Mai Girma Shugaban Ƙasa yana isa gare su ta wurina, saboda haka za su zaɓi Shugaban Ƙasa gaba dayansu” in ji gwamnan.

Kara karanta wannan
Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai
Gwamna Kefas ya hango nasarar Tinubu
Kun ji cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya ce APC za ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027, tare da tabbatar wa Tinubu cikakken goyon baya.
Gwamna Kefas ya kuma yi alƙawarin cewa Taraba za ta samar da kuri’u ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC “daga sama har ƙasa”.
Asali: Legit.ng
