Magana Ta Fito: An Ji Yadda Bankin Duniya Ya Jawo Aka Cire Tallafin Fetur a Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya ce Bankin Duniya ya bayyana yadda bankin duniya ya jawo cire tallafin mai
- Fashola ya ce cire tallafin ba matakin siyasa kawai ba ne, domin akwai tanadin doka da kuma matsin tattalin arziki da suka sa aka ɗauki matakin
- Ya kare gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan ƙin dawo da tallafin, duk da ƙalubalen tattalin arziki da hakan ya janyo wa 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya ce Bankin Duniya ne ya kafa wa Najeriya sharadin da ya tilasta cire tallafin man fetur.
Tsohon ministan ya ce Bankin Duniya ya shaida wa Najeriya cewa ba zai ƙara ba ta tallafin kuɗi ba idan har ba ta cire tallafin man fetur ba.

Source: Facebook
Fashola, wanda ya riƙe muƙamin ministan wutar lantarki a gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Kara karanta wannan
Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu
Dalilin cire tallafin fetur a Najeriya
Ya ce matakin cire tallafin man fetur ba zaɓin siyasa ba ne, domin yana da alaƙa da tanade-tanaden doka da kuma halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Fashola ya buƙaci 'yan Najeriya su sake nazarin jawabin rantsar da Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce hankalin jama'a ya fi karkata ne kan furucin shugaban cewa “an cire tallafi”, ba tare da la'akari da sauran abubuwan da ya faɗa a jawabin ba.
Ya ce Dokar Fetur (PIA) ta tanadi cewa ya kamata a sayar da kayayyakin mao bisa farashin kasuwa, yana mai cewa wannan tanadi yana da tasiri ga duk wani yunƙuri na dawo da tallafin.
Ya ce:
“Bankin Duniya ya fito fili ya fada mana cewa, ‘Ba za mu sake ba ƙasarku kuɗi ba sai kun cire tallafin.’ Haka kawai abin yake.”
Najeriya na biyan bashi mai yawa
Fashola ya ce an tattauna batun cire tallafin ne a lokacin gwamnatin da ta gabata, lokacin da yake cikin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Ya ƙara da cewa a lokacin, Najeriya na kashe kusan kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta wajen biyan basussuka.
Ya bayyana cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyin tallafin fetur ba, inda ya nemi waɗanda ke son a dawo da shi su bayyana inda za a samo kuɗin gudanar da shirin.
Tsohon ministan ya kuma ƙalubalanci 'yan adawar Tinubu da ke adawa da cire tallafin da su bayyana yadda za su aiwatar da wata manufar daban idan aka zaɓe su.
Fashola ya kare lafiyar Tinubu
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya ce bai ga wani abu da ke nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da lafiya ba.
Fashola ya bayyana cewa duk da tsufan Tinubu, hakan ba yana nufin hankalinsa ya ragu ba, domin har yanzu yana gudanar da ayyukansa.
Asali: Legit.ng
