An Tona Asirin Amurka kan Makaman da Ta Kawo Harin Sokoto da Su a 2025

An Tona Asirin Amurka kan Makaman da Ta Kawo Harin Sokoto da Su a 2025

  • Wani rahoto ya bayyana cewa Amurka ta yi amfani da makaman linzami na Tomahawk da wa’adin amfaninsu ya ƙare wajen kai hare-hare a Najeriya
  • An harba makamai 16 a wani samame na haɗin gwiwa tsakanin sojojin Amurka da Najeriya a jihar Sokoto a watan Disambar bara
  • Rahoton da aka fitar a kwanan nan ya ce huɗu daga cikin makaman sun kasa fashewa bayan sun isa wuraren da aka harba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani rahoto ya nuna cewa sojojin Amurka sun yi amfani da makaman linzami na Tomahawk da wa’adin amfaninsu ya ƙare wajen kai hare-haren ranar Kirsimeti kan mayakan ƙungiyar IS a Najeriya.

An samo bayanin ne daga wani jami’in Amurka da ke da masaniya kan aikin sojan, a cikin rahotonta kan ƙarancin wasu muhimman makaman yaƙi da rundunar sojojin ruwan Amurka ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya fara garkuwa da mutane a Amurka, 'yan sanda na neman shi

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda Amurka ta kai hari Sokoto

Wall Street Journal ta ce rahoton ya fito ne yayin zaman tantance Hung Cao, wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya zaɓa domin jagorantar rundunar sojojin ruwan ƙasar.

A yayin zaman a ranar Talata, Cao, wanda tsohon kyaftin ne a rundunar sojojin ruwan, ya bayyana cewa rundunar na amfani da makaman Tomahawk da wa’adin amfaninsu ya ƙare a Gabas ta Tsakiya.

Ya ce rundunar ta samu damar sake tsara bayanan fasahar makaman, domin su koma cikin waɗanda za a iya amfani da su a yaƙin Iran.

Dalilin da ya sa ake duba wa’adin makaman

Mark Montgomery, wani tsohon babban jami’in rundunar sojojin ruwan Amurka ya bayyana cewa rundunar na sanya wa makamai wa’adin amfani ne saboda wasu daga cikinsu kan fara samun matsalolin fasaha bayan sun tsufa.

Rahoton Press Tv ya nuna cewa ya ce ana iya sake tantance makaman domin tabbatar da cewa har yanzu suna iya aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Matashi ya mutu a ƙoƙarin kare iyayensa daga sharrin 'yan bindiga

Hakan na faruwa ne bayan an gudanar da bincike da gwaje-gwaje domin tabbatar da cewa ingancin makamin bai lalace ba.

Rahoton ya ce Amurka ta yi amfani da wannan dabarar wajen shirya makaman Tomahawk da ta harba kan mayakan ’yan ta’adda a jihar Sokoto a watan Disambar bara.

An harba makamai 16 a Najeriya

Aikin sojan na haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya ya yi amfani da makaman Tomahawk guda 16.

A lokacin, an samu rahotannin cewa huɗu daga cikin makaman sun isa wuraren da aka nufa amma ba su fashe ba.

Wasu mazauna yankin sun ce ɗaya daga cikin makaman ya faɗa gonar albasa a ƙauyen Jabo, jihar Sokoto.

Jabo da aka kai hari a Sokoto
Wajen da Amurka ta kai hari a Sokoto. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

An kuma ce wani ya faɗa kan gine-ginen zama a Offa, jihar Kwara, yayin da na uku ya faɗa wani gonar noma a wajen Offa.

Trump ya yi magana kan Kim

A wani labarin, mun rahoto cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan yiwuwar ganawa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, a lokacin ziyarar da ya kai ƙasashen Asiya.

Kara karanta wannan

Yadda sojojin Amurka ke aiki da Najeriya gabanin zaben 2027

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a birnin Manila na ƙasar Philippines a ranar 17 ga Nuwamba, inda ya ce yana ganin Kim Jong-un ma zai so ganawa da shi.

Tun a ranar 16 ga Nuwamba, kafin ya bar fadar White House domin tafiyar ƙasashen waje, Trump ya bayyana cewa yana iya ganawa da Kim Jong-un, tare da shugabannin China da Rasha, Xi Jinping da Vladimir Putin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng