Tinubu Ya Gargadi 'Yan Siyasa bayan kai wa Pantami da 'Yan NDC Hari

Tinubu Ya Gargadi 'Yan Siyasa bayan kai wa Pantami da 'Yan NDC Hari

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da karuwar tashe-tashen hankula a harkokin siyasa a sassan Najeriya
  • Tinubu ya gargadi 'yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani hali na rashin da'a yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • A bayanin da ya yi, shugaban kasar ya ce ba za a lamunci duk wani rashin da'a daga 'yan siyasa da magoya bayansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da karuwar rikicin siyasa a sassan Najeriya, inda ya bukaci jami’an tsaro su dauki tsauraran matakai kan duk wanda ke kokarin tada tarzoma.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Juma’a, inda ya bukaci shugabannin siyasa da magoya bayansu daga dukkan jam’iyyu su nuna halin dattaku.

Kara karanta wannan

An yi wa Tinubu ihun 'ba ma yi' da ya je masallacin Juma'a a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi ga 'yan kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A sakon da Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook, Tinubu ya ce ya kamata yakin neman zabe ya mayar da hankali kan manufofi da musayar ra'ayoyin da za su inganta rayuwar jama'a da ci gaban kasa.

Tinubu ya yi tir da rikicin siyasa

Shugaban kasar ya ce ya lura da rahotannin tashin hankali da ake samu a wuraren gudanar da harkokin siyasa a sassa daban-daban na Najeriya.

Ya ce duk wani nau'i na tashin hankali abin Allah wadai ne, kuma bai kamata ya samu gurbi a yakin neman zaben 2027 ba.

Tinubu ya ce:

“Na sha bayyana cewa kasancewa a jam’iyyun siyasa daban-daban ko kuma neman cimma muradun siyasa daban-daban ba yana nufin mu zama makiya ba.
“A matsayinmu na ’yan Najeriya, muna cikin gida daya ne, sai dai muna zaune a dakuna daban-daban. Don haka, ya kamata siyasa ta mayar da hankali kan inganta rayuwar al’umma da ci gaban kasa.”

Kara karanta wannan

Na gaban goshin Tinubu ya fadi wanda suke shakka a 2027, ban da Atiku da Obi

Tinubu ya gargadi 'yan siyasa

Daily Trust ta rahoto cewa Tinubu ya sake jaddada kudurinsa na ganin an gudanar da zabe cikin lumana, 'yanci da adalci.

Ya bukaci shugabannin siyasa da magoya bayansu su nuna halin dattaku, tare da gujewa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Ya kuma ce dukkan jam’iyyun siyasa da 'yan takararsu ya kamata su samu damar gudanar da yakin neman zabe a duk inda suke so a fadin kasar ba tare da tsangwama ko fargabar barazana ga rayukansu ba.

Tunji Disu a bakin aiki
Sufeton 'yan sanda, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Shugaban kasar ya sake jaddada umarnin da ya bai wa hukumomin tsaro a baya na su dauki tsauraran matakai kan duk wanda ya yi kokarin kawo cikas ga zaman lafiyar jama'a.

Ya ce:

“Ba za mu lamunci duk wani hali na rashin da'a daga 'yan siyasa da magoya bayansu ba.
“Saboda haka, an ba jami’an tsaro izinin fuskantar daba da sauran ayyukan rashin zaman lafiya da suka saba wa dimokuradiyya da cikakken karfi.”

Kara karanta wannan

Ana rikicin ADC, Nafiu Bala ya fito da maganganu kan Tinubu da Atiku

An kai wa Pantami hari

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da harin da wasu 'yan daba suka kai wa tawagar yakin neman zaben PDP a jihar Gombe ranar 11 ga Nuwamba, 2026.

Kungiyar ta ce tana zargin wasu da hannu a jam'iyyar APC da kai harin, inda ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

A daya bangaren kuma, rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce ba ta kama wani mutum ba dangane da harin kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng