Yadda Gwamnatin Tinubu, Jihohi da Kananan Hukumomi Suka Raba N2.4trn

Yadda Gwamnatin Tinubu, Jihohi da Kananan Hukumomi Suka Raba N2.4trn

  • Kwamitin FAAC ya raba Naira tiriliyan 2.441 ga matakan gwamnati uku a watan Oktoban shekarar 2026
  • Gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 856.065, jihohi suka karɓi biliyan 809.909, yayin da ƙananan hukumomi suka samu biliyan 568.701
  • Kuɗaɗen shiga daga harajin VAT sun kai Naira biliyan 812.446, yayin da kuɗaɗen shiga na doka suka kai tiriliyan 2.999 a watan Oktoba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kwamitin raba kuɗaɗen shiga na tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.441 ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi a matsayin kuɗaɗen shiga na watan Oktoba 2026.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF), Bawa Mokwa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

"Mun shirya": Gwamna ya yi alkawarin samar da kuri'u miliyan 2 ga Tinubu a 2027

FAAC ya raba kudade
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Mokwa ya ce an raba kuɗaɗen ne a taron FAAC na watan Nuwamba 2026 da aka gudanar a Abuja, kamfanin dillacin labarai na NAN ya kawo rahoton.

Yadda aka samu kuɗaɗen da aka raba

A cewarsa, jimillar kuɗaɗen da aka raba ta ƙunshi Naira tiriliyan 1.688 daga kuɗaɗen shiga na doka, da kuma Naira biliyan 752.488 daga harajin kayayyaki da ayyuka (VAT).

Sanarwar taron FAAC ta nuna cewa jimillar kuɗaɗen shiga da aka samu kafin cire kuɗaɗen gudanarwa a watan Oktoba ta kai Naira tiriliyan 3.811.

An cire Naira biliyan 128.797 domin biyan kuɗaɗen karɓo kuɗaɗen shiga, yayin da aka ware Naira tiriliyan 1.241 domin canja wurin kuɗi, mayar da wasu kuɗaɗe da kuma ajiyar kuɗi.

Mokwa ya bayyana cewa kuɗaɗen shiga na doka kafin raba su sun kai Naira tiriliyan 2.999 a watan Oktoba. Wannan ya nuna raguwar Naira biliyan 97.323 idan aka kwatanta da tiriliyan 3.096 da aka samu a watan Satumba.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Haka kuma, kuɗaɗen shiga daga VAT sun kai Naira biliyan 812.446, wanda ke nuna raguwar Naira biliyan 4.426 daga biliyan 816.872 da aka samu a watan da ya gabata.

Nawa kowace gwamnati ta samu?

Bayan raba kuɗaɗen, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 856.065, yayin da gwamnatocin jihohi suka karɓi Naira biliyan 809.909.

Ƙananan hukumomi kuwa sun samu Naira biliyan 568.701. Bugu da ƙari, an ware Naira biliyan 206.384 ga jihohin da ake hakar ma’adanai, a matsayin 13% cikin 100% na kuɗaɗen shiga daga albarkatun ma’adanai.

Mokwa ya ce daga cikin Naira tiriliyan 1.688 na kuɗaɗen shiga na doka, gwamnatin tarayya ta samu biliyan 780.816, jihohi suka karɓi biliyan 396.040.

Ƙananan hukumomi sun samu Naira biliyan 305.331, yayin da jihohin da suka cancanta suka raba Naira biliyan 206.384 a matsayin 13% cikin 100% na kuɗaɗen albarkatun ma’adanai.

Dangane da Naira biliyan 752.488 na kuɗaɗen VAT, gwamnatin tarayya ta samu biliyan 75.249, jihohi suka karɓi biliyan 413.868, sannan ƙananan hukumomi suka samu biliyan 263.371.

Kwamitin FAAC ya raba kudade
Naira 100 a cikin kudaden tarayyar Najeriya Hoto: @cenbank
Source: Instagram

FAAC ya raba kudade

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin raba kuɗaɗen shiga na tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.43 ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi a watan Satumban 2026.

Daga cikin kuɗaɗen da aka raba, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 832.24, yayin da jihohi suka samu Naira biliyan 799.87.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng