Rokicin NNPP: An Sake Kunno Wa Kwankwaso Wuta bayan Gwamna Abba Ya Koma APC
- Rikicin jam'iyyar NNPP ya dauki sabon salo bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano tare da mukarrabansa
- Tsagin NNPP da ke goyon bayan shugabancin Agbo Major ya soki masu ayyana Kwankwaso a matsayin jagoran jam'iyya na kasa
- Mataimakin shugaban NNPP na Arewa maso Yamma, Sani Danmasani ya ce suna da hujjojin da ke tabbatar da an kori Kwankwaso daga jam'iyya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsagin jam’iyyar NNPP da ke goyon bayan Dr. Agbo Major ya sake taso tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewar bangaren NNPP, Kwankwaso ba shi ne jagoran jam'iyyar a jihar Kano ko a matakin kasa ba kamar yadda ake yadawa musamman a kafafen yada labarai.

Source: Facebook
Tsagin NNPP ya yi fatali da Kwankwaso

Kara karanta wannan
Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito
Vanguard ta rahoto cewa wannan bayani ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban NNPP na Yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Sani Danmasani, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Danmasani ya ce ficewar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP ba ya nufin cewa Kwankwaso da mabiyansa 'yan Kwankwasiyya sun dawo cikin jam’iyyar saboda an dade da korarsu.
“Abba yana daga cikin jagororin NNPP a baya, amma jagoran jam’iyyarmu shi ne wanda ya kafa ta kuma shi ne shugaban Kwamitin Amintattu, Boniface Aniebonam,” in ji Danmasani.
Matsayin Kwankwaso a jam'iyyar NNPP
Ya bayyana matuƙar mamakinsa kan yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke ci gaba da kiran Kwankwaso a matsayin jagoran NNPP, alhali a cewarsa an kore shi daga jam’iyyar tun tuni.
“Abin mamaki ne yadda yawancin kafafen watsa labarai ke ci gaba da kiran Kwankwaso a matsayin jagoran NNPP, jam’iyyar da ya ci amanarta kuma har yanzu yana ƙoƙarin ƙwace ta duk da cewa an kore shi,” in ji shi.
Danmasani ya ce NNPP na da cikakkun hujjoji na doka da za su iya nuna wa manema labarai cewa ta kori Kwankwaso da wasu mutane kamar Ahmed Ajuji da Buba Galadima daga jam’iyyar bisa ƙa’idojin ladabtarwa na cikin gida.
Da gaske NNPP ta kori Kwankwaso?
Ya ƙara da cewa babbar kotun jihar Abia da kuma Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja sun tabbatar da korarsu ta hanyar doka, kamar yadda jaridar Guardian ta kawo.

Source: Facebook
A cewarsa, kotun tarayya da ke Abuja ta yi umarnin hana hukumar INEC mu’amala ko gudanar da wata harkar jam’iyya da Kwankwaso ko kwamitin NWC ƙarƙashin Ajuji, har sai an kammala shari’a.
Ya bayyana cewa da zarar INEC ta kammala nazari da kuma bita na shari’a, za a ɗora sunayen Dakta Agbo Major da Mista Oginni Olaposi, a matsayin shugabannin NNPP a shafin hukumar.
Kwankwaso ya ci amanar Hamisu Musa?
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayani kan zargin da ake cewa ya ci amanar Sanata Hamisu Musa a siyasance.
Kwankwaso ya bayyana cewa bai taba cin amanar Sanata Hamisu Musa ba kamat yadda ake yadawa ba, yana mai cewa karamin sabani ne ya shiga tsakaninsu.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tun daga wannan sabani mutane da dama, ciki har da Sarkin Dawaki, sun shiga tsakani domin a sasanta su, amma Sanata Hamisu Musa ya ki hakura.
Asali: Legit.ng
